Karin Bayani: Abin da ke Faruwa a Sudan Kawo Yanzu!

 

Yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da aka cimma a Sudan – tsakanin ɓangarorin da ke faɗa wato sojojin ƙasar da kuma dakarun RSF za ta kawo karshe a daren yau. Ana ci gaba da faɗa a sassan ƙasar duk da cimma yarjejeniyar.

Ma’aikatar lafiya a Sudan ta ce akalla mutum 512 ne aka kashe a rikicin kawo yanzu, tun baya ɓarkewar faɗa a rabar 15 ga watan Afrilu. Sai dai ana tunanin cewa alkaluman za su iya fin haka.

Kusan ƴan Birtaniya 536 aka kashe daga Sudan. BBC ta tattauna da mutane da ke isa filin jirgin Larnaca da ke Cyprus.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya James Celeverly ya bai wa ƴan ƙasar da ke Sudan shawarar cewa su fice nan take.Ya ce babu tabbacin cewa za a iya ci gaba da aikin kwashe mutane bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta.

BBC ta samu rahotanni da ke cewa mayaƙa na ci gaba da addabar fararen hula a birnin Nyalain a kudancin yankin Darfur, abu kuma da ke nuna cewa rikcin ya yaɗu zuwa wajen Khartoum, babban birnin ƙasar.

Motocin bas ɗauke da wasu daga cikin ɗaliban Najeriya ya tashi daga Sudan a jiya Laraba, inda ya nufi ƙasar Masar.

Haka nan ma sauran ƙasashe da dama na ci gaba da kokarin kwashe ƴan ƙasarsu da ke Sudan a daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta ta kwanaki uku ke kawo karshe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here