Marburg: Abubuwa 4 Game da Sabuwar Cutar da ta Shigo Afrika

 

Cutar Marburg ta samo asali ne daga biranen Marburg da Frankfurt da kuma Belgrade a kasar Yugoslavia a shekarar 1987.

A cewar WHO, cutar ta samo asali ne daga jemagu.

An fara gano cutar Marburg ne a 1967, inda mutane 31 sukayi rashin lafiya a Jamus da Yugoslavia inda aka gano cewa akwai cutar jikin birai a Uganda.

Legit tattaro muku abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da wannan cuta:

1. Tana iya bazuwa tsakanin mutum zuwa mutum

A cewar WHO, cutar ta samo asali ne daga cikin jemagu kuma tana iya bazuwa tsakanin mutum zuwa mutum ta zufar jiki ko idan yawun mutum ya fada kan abubuwa.

Idan mutum ya taba wani abu da kwayar cutar ta fada kai, mutum na iya kamuwa.

2. Adadin mutane mafi yawa da suka mutu sakamakon cutar a shekara shine 227

A cewar Wikipedia, tun lokacin da cutar ta bulla a 1967, adadin mutanen da ta hallaka a shekara guda 227.

Mutum 227 sun mutu a shekarar 2004-2005 a Angola. Bayan haka garin Durba da Watsa, a kasar Congo ta yi rashin mutum 128 tsakanin 1998-200.

3. Alamomin kamuwa da cutar

A cewar WHO, alamomin kamuwa da cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, gudawa, ciwon mara. Wanda ya kamu da cutar cikin kwanaki bakwai, ana iya ganin jini cikin amansa da ba haya.

4. Babu maganin cutar

Kawo yanzu, babu rigakafin wannan cuta kuma babu maganinta, illa yan magunguna da ake baiwa masu fama da ita don rage radadi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here