Bola Tinubu ya Mika Sakon Godiyarsa ga Shugaba Buhari Kan Ziyarar da ya Kai Masa a Landan

 

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya nuna godiya ga shugaba Buhari kan ziyarar da ya kai masa.

Buhari a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta ya ziyarci Tinubu a Landan yayin da ake rade-radin cewa shugaban na APC yana fama da rashin lafiya.

Tsohon gwamnan na jahar Legas ya ce ziyarar da Buhari ya kai ta nuna halinsa na kulawa.

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu, ya nuna matukar godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ziyarar da ya kai masa a Landan a ranar 12 ga watan Agusta, jaridar Thisday ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa shugaba Buhari ya yi a ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, ya ziyarci Tinubu a lokacin da yake kasar Ingila.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa daga ofishin yada labarai na jiya ya ce:

“Ziyarar ta sada zumunci ce kuma abun so wacce ta jaddada mutunci da kulawar Shugaban kasarmu kuma Babban Kwamandan mu.

“Da wannan karimcin, Shugaban kasa ya sake nuna irin tunaninsa da tawali’u; ya bijirewa sharhin da masu sukarsa suka yi.

“Asiwaju yana sake godewa Shugaba Buhari da ya dauki lokaci don ya ziyarce shi kuma baya yiwa Shugaban kasar fatan komai face na alkhairi yayin da gwamnatinsa ke ci gaba da gudanar da mulki da jagorancin al’umma.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here