Abubuwan da ke Kawo Tangarɗa a Yunƙurin Inganta Wutar Lantarki a Najeriya
Wata matsala da ƴan Najeriya ke fama da ita tsawon shekaru ita ce rashin tsayayyiyar wutar lantarki abin da ke shafar harkokin yau da kullum da kuma na kasuwanci.
Sai dai matsalar ta yi muni a baya-bayan nan inda ake samun yawan ɗaukewar lantarki a faɗin ƙasar ko ma rashin wutar na tsawon kwanaki a wasu jihohin duk da kasancewar ƙasar babbar mai samar da iskar gas da man fetur ce.
Lamarin kuma ya zo a daidai lokacin da ake fuskantar yanayi na tsananin zafi sannan kuma al’ummar musulmi a ƙasar ke azumin watan Ramadan – wani lokaci da mutane ke buƙatar wuta sosai domin samun kayan sanyaya maƙoshinsu a lokacin bude baki.
Rashin wutar kan janyo lalacewar abinci cikin sauri musamman wanda aka ajiye a firinji, sai kuma yadda matsalar ta janyo durƙushewar harkokin kasuwanci.
Hukumomi dai sun sha cewa suna aiki domin magance matsalar da suke alaƙantawa ga matsalar ƙarancin iskar gas da ke samar da kashi 80 cikin 100 na wutar da kuma ayyukan masu satar kayan wuta a cibiyoyin wuta da ke faɗin ƙasar.
A watan Nuwamban 2022, Najeriya ta iya cimma yawan karfin lantarki megawatts 4,594.6.
Matsalar ta sa mutane da dama nemarwa kansu mafita ta hanyar komawa amfani da wutar sola mai amfani da hasken rana wasu kuma suna amfani da injin janareto.
Ƴan Najeriya da dama sun bayyana rashin jin daɗinsu ga yadda matsalar wutar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
Lamarin da ya sa wasu ƴan Najeriyar zuwa shafukansu na sada zumunta domin bayyana yadda matsalar ta kai masu maƙura inda suke caccakar hukumomi tare da neman su yi bayanin abin da ke sa ake yawan ɗauke wuta a ƙasar.
Stein wani ma’abocin shafin X da aka fi sani da Twitter a baya, inda ya wallafa cewa babu wani abu da ke tafiya daidai a Najeriya har da wutar lantarki da sadarwar intanet.
Ita ma Boss Lady a shafinta na X ta bayyana cewa “duk lokacin da Ramadan ya zagayo, sai an samu ƙarancin wutar lantarki a Najeriya.”
Read Also:
Kaɗan daga cikin irin ƙorafe-ƙorafen da ƴan Najeriya ke yi game da matsalar rashin wutar.
Wannan ne kuma ya sa za mu duba abin da ke janyo matsalar wutar da kuma hanyoyin da ya kamata hukumomi su bi domin daidaita al’amura tare da magance matsalar da kuma yawan wutar da ake buƙata Najeriya ta fita daga ƙangin na rashin wutar.
Najeriya ta gaza samar da isasshiyar wuta
Injiniya Yabagi Sani, masani kan harkar makamashi ya ce matsalar rashin wuta a Najeriya ta zama abin damuwa.
Ya ce gwamnati ta saka isasshen kuɗin da ya kamata wajen inganta ɓangaren wutar lantarki.
“Halin da aka shiga da aka cire tallafin mai, gwamnati ba za ta iya fitowa ta ce an cire tallafin da ake bayar wa a ɓangaren wutar lantarki ba.”
“Ke nan gwamnati ta kasa domin ba ta da kuɗin kuma rashin kuɗin ya sa abin da ke buƙata domin yin gyara a ɓangarorin samar da wutar lantarkin.” in ji shi.
Masanin ya ce har yanzu Najeriya ba ta samar da rabin ƙarfin wutar da ya kamata ta rika samarwa ba, kasancewar a yanzu tana iya samar da megawatt dubu 13 kawai.
“Abin da muke buƙata da zai samar da isasshiyar wuta a Najeriya ya kai megawatt dubu 25.” kamar yadda ya ce.
Injiniya Yabagi ya kuma yi magana kan abubuwan da ke kawo tangarɗa a yunƙurin inganta wutar lantarki a ƙasar.
Ya lissafo dalilai biyu da ke janyo wannan matsala – ayyukan ƴanbindiga da ke kai hare-hare kan cibiyoyin lantarki.
Sai kuma matsalar cin hanci da rashawa inda ake samun kuɗaɗen da ake warewa don inganta wuta ke zurarewa ta wannan hanya.
Yadda za a shawo kan matsalar
Injiniya Yabagi Sani ya bayyana cewa akwai hanyoyi da dama da gwamnati ya kamata ta bi domin samar da wutar lantarki mara ɗaukewa.
Ya lissafo hanyoyin kamar haka:
Zuba isasshen kuɗi domin yin gyaran da ake buƙata a ɓangaren lantarki
Ƙara yawan iskar gas da ya kamata a yi amfani da ita don samar da wuta
Ƙara kaimi wajen ƙara yawan megawatts ɗin da ake samarwa
Maganin matsalar cin hanci da rashawa da ta yi katutu
A cewarsa, matuƙar gwamnati ta warware waɗan nan matsalolin, to talaka a Najeriya zai samu sauƙin rashin wuta.