Abubuwan Alherin da na yiwa Al’ummar Jahar Kebbi – Abubakar Malami
Dan takaran gwamnan Kebbi ya lissafa jerin abubuwan alherin da ya yiwa al’ummar jihar da yake son mulka.
Abubakar Malami yace yanzu yana kokarin mayar da mutum 500 masu kudi miloniya.
Malami, wanda shine Ministan Shari’a ya jaddada karyata rahotannin cewa ya rabawa deleget motoci.
Read Also:
Birnin-Kebbi – Antoni Janar na tarayya kuma dan takaran kujerar gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Malami, ya ce ta dalilinsa mutum sama da 500 sun zama miloniya a jihar.
Malami ya bayyana hakan ne a gidansa dake Birnin Kebbi yayinda ya karbi bakuncin kungiyar magoya bayansa makon da ya gabata, rahoton PremiumTimes.
Ya kara da cewa ya samawa matasa sama da 700 ayyuka.
A cewarsa:
“Mun samu nasarar samawa mutum 700 ayyukan yi. Mun gina rijiyar burtatsai sama da 200 a fadin jihar, muna taimakawa jihar wajen mayar da mutane 500 miloniya a jihar.”
“Mun taimakawa sama da mutum 6000 wadanda suka samu tallafin COVID-19 kowanne N550,000.”