Adadin Mutanen da Suka Kamu da Cutar Korona Ranar Laraba
Ta tabbata yanzu, annobar korona ta sake waiwaye a karo na biyu a Najeriya.
Gwamnati ta bada umurnin rufe makarantu, gidajen biki, gidajen rawa dss.
An sake dokar kulle a jihar Kwara amma Plateau ta ce ba zata rufe jama’a ba.
Alkaluma akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria sun nuna cewa ko shakka babu angulu ta koma gidanta na tsamiya.
Read Also:
Mutane 1133 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.
Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 80,9222 a Najeriya. Daga cikin sama da mutane 80,000 da suka kamu, an sallami 69,274 yayinda 1236 suka rigamu gidan gaskiya.
Ga jerin jiha-jiha:
Lagos-397
FCT-357
Kaduna-81
Plateau-63
Katsina-46
Sokoto-32
Oyo-28
Ogun-21
Kano-19
Rivers-18
Osun-13
Edo-12
Niger-12
Bayelsa-11
Borno-11
Bauchi-8
Jigawa-2
Ondo-2