2023: Wata Kungiya ta Shawarci Wani Gwamna da ya Nemi Kujerar Shugaban Kasa

An bukaci Gwamna Bala Mohammed ya duba yiwuwar fitowa tseren kujerar shugaban kasa a 2023.

Wata kungiya a Abuja ce ta shawarci gwamnan na Bauchi a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin.

An bayyana Bala Mohammed a matsayin shugaba mai tarin sani wanda ka iya cimma mafarkin kasar.

Wata kungiyar jama’a ta gamayyar matasa da mata, ta yi kira ga Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na jihar Bauchi da ya fito takarar kujerar Shugaban kasa a 2023.

Kungiyar ta yi kiran ne a cikin wata takarda da ta saki a karshen taronta a Abuja, a ranar Litinin dauke da sa hannun Aminu Zakari da Christiana Jacob, shugaba da sakatariyar kungiyar.

A cewar kungiyar, zuwa 2023, Najeriya za ta kasance cikin tsananin bukatar shugaba mai gaskiya da cancanta domin jagorantar harkokin kasar.

Har ila yau kungiyar ta ce yan Najeriya na bukatar shugaba da zai kare kasar daga hargitsi da durkushewa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here