Adadin Mutanen da Cutar Kansa ke Kashewa a Duk Shekara a Nahiyar Afrika – Hukumar Lafiya ta Duniya

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce a kowacce shakara akan samu kusan mutum miliyan 1.1 da ke kamuwa da cutar Kansa a nahiyar Afirka inda kusan mutum 700,000 ke mutuwa sakamakon cutar.

Daraktar hukumar mai lura da kasashen Afirka Dakta Matshidiso Moeti, ce ta bayyana haka ranar Lahadi a wani jawabi da ta gabatar a bikin ranar yaƙi da cutar ta duniya mai taken ‘Inganta Hanyoyin Yaki da Cutar: Mu haɗa muryoyinmu domin ɗaukar mataki’.

Ta ce hasashen da aka yi yanzu na nuna cewa akwai barazanar samun kashi 50 cikin ɗari na yaran da ake haihuwa da cutar a nahiyar Afirka zuwa shekarar 2050.

Ta ƙara da cewa alkaluman sun nuna cewa akwai hasashen samun ƙaruwar mace-mace sakamakon cutar kansa zuwa kusan miliyan ɗaya a kowacce shekara zuwa 2030, idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba.

Dakta Moeti ta ce ƙasashe 12 ne a nahiyar Afirka ke da kyakkyawan shirin yaƙi da cutar.

Jami’ar ta WHO ta ce Hukumar na taimaka wa ƙasashe 11 domin samar da ko inganta shirye-shiyensu na yaƙi da cutar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here