Da Gangan Emefiele ya Aiwatar da Manufar Sauya Kudi Cikin Dan Kankanin Lokaci – Ganduje

 

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya zargi gwamnan CBN, Godwin Emefiele, da kokarin haddasa rudani a zaben 2023.

Ganduje ya ce Emefiele ya sauya kudin Najeriya a daidai wannan lokaci ne saboda haushin bai samu tikitin takarar shugaban kasa a APC.

ba Yayin da take bayyana cewa bata goyon bayan sauya kudi a yanzu, gwamnatin Kano ta ce za ta rabawa mutane kayan rage radadi a fadin kananan hukumomi 44.

Kano – Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya yi ikirarin cewa da gangan gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya aiwatar da manufar sauya kudi cikin dan kankanin lokaci.

Ganduje ya ce Emefiele ya yi hakan ne saboda haushin gaza samun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressive Congress (APC).

Ya bayyana hakan ne a wajen yakin neman zaben jam’iyyar wanda ya gudana a Tsanyawa a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairu, jaridar Punch ta rahoto.

A wajen gangamin kamfen din ne gwamnan na Kano ya gabatar da dan takarar gwamnan APC, mataimakinsa da sanatocin jam’iyyar da sauransu ga mutanen jihar.

A cewar wata sanarwa da sakataren labaran gwamnan, Abba Anwar, ya saki, Ganduje ya ce:

“Gwamnan na CBN na aikata hakan ne kawai don haddasa rudani a zabe mai zuwa saboda wasu dalilai marasa tushe.

“Tsawon lokaci yanzu, gwamnan na CBN yana cikin bakin ciki saboda gaza samun tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyarmu mai albarka ta APC.”

Gwamnatin Kano bata tare da Emefiele, Ganduje

Gwamna Ganduje ya fito karara ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano da jam’iyyar APC a jihar basa tare da wannan mataki na gwamnan CBN, rahoton Daily Post.

Ya ci gaba da cewa:

“Sauya kudi abu ne da ake yi a fadin duniya, amma ba yadda muke fuskanta a kasarmu ba. Lokacin bai dace ba, wa’adin da aka bayar baya bisa daidai kuma da gangan aka yi haka.”

Gwamnan na Kano ya jero wasu matakai da za su dauka don saukaka mawuyacin halin da sauya kudin ya jefa mutane a ciki kaar haka:

“Za mu sammaci manajojin bankiu nan ba da jimawa ba don yi masu tambayoyi kan karancin sabbin kudi a bankuna.

“Ya kamata su zo nan sannan su yi mana bayani, menene dalilin da yasa mutanenmu ke shan wahala kan wannan lamari na sauya naira. Zan ziyarce su da kaina don sanya ido kan abun da ke faruwa da dalili.”

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here