Hukumar NDLEA ta Kama Mai Juna Biyu Kan Kokarin Safarar Miyagun Kwayoyi

 

Wata mata mai dauke da juna biyu ta fada komar NDLEA bayan da tayi kokarin safarar miyagun kwayoyi.

Matar wanda ta kunshe wiwi a cikin kananan rediyo guda biyu, tayi nufin aika kayan Dubai kafin ta shiga hannu.

Jami’an NDLEA na ci gaba da yunkuri wajen dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi kamar yadda kakin su na Lagos ya bayyana.

Legas – Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke sansanin fita da kaya ta NAHCO shiyyar filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad, da ke Ikeja, Lagos, sun kama wata mata mai juna biyu, Mrs Sylvester Gloria Onome, ranar Litin, 30 ga watan Janairu, 2023, saboda samun ta da miyagun kwayoyi.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ranar Lahadi a Abuja ya ce an kama matar da giram 800 na wiwi da aka boye a cikin kananan rediyo da za a tura Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa, rahoton Vanguard.

Duk a ranar, Hukumar NDLEA ta kuma dakatar da wasu kayan da aka tura jamhuriyyar Congo, Kinshasa, dauke da kwalabe 111 da mayukan shafawa da aka boye kilo 24.50 na ephedrine, wani sinadari da ake amfani da shi wajen hada methamphetamine.

Babafemi ya ce:

”An bibiyi sahun kayan inda aka kama wani dan tireda a kasuwar bajakolin Alaba, dake yankin Ojo a Lagos, Onyekachukwu Uduekwelu, bayan damke wasu jami’an tura kaya biyu tun da fari”

An kama wata matar aure dauke da miyagun kwayoyi

A ranar Juma’a, 27 ga Janairu, an kama wata matar auren, Mrs Okpara Chizoba Victoria, a gidan ta mai lamba 37, Obashola street, a yankin Ijesha na Jihar Lagos, bayan kwace giram 300 na wiwi da aka boye a jakar busasshen kifi da za a aika Dubai, hadaddiyar daular larabawa ta hannun jami’in aika sako.

Haka hukumar ta dakile safarar wasu miyagun kwayoyi masu yawa, musamman hodar iblis, heroin, methamphetamine da ephedrine da za a tura Dubai, UAE da kuma nahiyar turai ta hanyoyin basaja da yawa daga wajen manyan dilolin miyagun kwayoyi ta MMIA dake Ikeja a Lagos, jami’an NDLEA sun yi nasarar dakile wa tare da kama masu laifin.

A cewar rahoton The Cable, daga cikin manyan da suka hannu akwai wani dan Najeriya mazaunin Athens, a kasar Greece, Iwuodur Edward Chinedu.

Ya fada komar hukuma ne a jirgin Ethiopian airline ranar Juma’a, 3 ga Fabrairu, bayan da jami’an NDLEA na filin jirgi suka wasu jakunkuna biyu lokacin gudanar da binciken da ake kafin hawa jirgi.

Lokacin da ake bincika jakar a gaban Chinedu da sauran jami’an filin jirgi, an samu wasu manyan curi guda biyu an nade su da takardar foil da kuma barkono da aka warwatsa a saman jakar da kowanne bangaren jakar.

An yi amfani da curin don tsayar da jakar kuma an samu wasu kayyayaki da ke dauke da hodar iblis da kuma heroin da nauyin su ya kai kilo 1.30 da kuma giram 900, kowanne.

A cewar Babafemi:

”Yayin da yake amsa tambayoyi, Chinedu ya ce ya zo Najeriya ne wata uku da suka gabata domin ayi masa tiyata, wadda shi bai yadda anyi masa a Athens ba. Ya kuma ce an bashi jakar ne don ya kai kasar Greece akan kudi Naira miliyan 2.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here