Adadin Mutanen da Aka Kashe da Kuma Wanda Akai Garkuwa da su a Watan da ya Wuce

Akalla mutane 349 aka hallaka a watan Nuwamba a hare-hare a fadin Najeriya, rahoton wata kungiya mai zaman kanta, Nigeria Mourns, ya nuna.

Rahoton mai taken “Rahoton hare-hare: Nuwamba 2020,” ya bibiyi kashe-kashen da akayi a fadin tarayya.

Kungiyar na amfani da rahotannin jaridu da bayanin iyalai domin tattara bayananta.

A cewar rahoton, an kai hare-hare jihohi 23 a watan Nuwamba.

Lissafin ya nuna cewa cikin mutane 349 da aka kashe, 309 masu farin hula ne yayinda 40 jami’an tsaro.

Hakazalika, an yi garkuwa da mutane 290 a watan Nuwamba.

Jihar Borno a Arewa maso gabashin Najeriya, wacce ke fuskantar ta;’addin Boko Haram, ce ta debi kaso mafi yawa na wadanda aka kashe.

Bayan jihar Borno, yadda aka samu kashe-kashe a jihohin Najeriya ya nuna cewa matsalar tsaro bai kebanta ga wanin sashen Najeriya ba.

Misalin jihar Edo ta biyo jihar Borno na adadin mutanen da aka hallaka a Nuwamba.

Ga jerin jihohin da adadin wadanda suka rasa:

Borno – 162, Edo – 57, Kaduna – 55, Katsina -12, Delta – 11, Zamfara – 10, Oyo – 5, Ondo – 5, Enugu – 4, Kogi -3, Kano – 3, Ekiti – 3, Adamawa – 3, Bayelsa – 3, Cross River – 2, Nasarawa – 2, Niger – 2, Rivers – 2, FCT – 1, Akwa Ibom – 1, Ebonyi – 1, Ogun – 1 and Sokoto – 1. Game da wadanda sukayi wannan kashe-kashe, rahoton ya nuna cewa yan ta’addan Boko Haram suka kashe 149; yan bindiga sun hallaka 86; yayinda rikicin yan daba yayi sanadiyar rayukan 62.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here