Yadda Hadimin Ministan Sadarwa ya Kubuta a Hannun Masu Garkuwa

Wani jami’in dan sanda kuma dogarin Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pantami, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane amma ya samu kubuta.

Dan sandan, wanda dan asalin jihar Nasarawa ne, yana kan hanyar zuwa Abuja daga Doma a karshen makon da ya gabata akayi garkuwa da shi a Ikari, wani kauye dake Gudi karkashin karamar hukumar Akwangaa jihar Nasarawa.

Wani mai idon shaida ya ce wannan abu ya faru ne misalin karfe 8 na dare yayinda yan bindigan suka tare hanya, suka yi fashi, sannan sukayi awon gaba da mutane hudu.

Ya ce an tura yan sanda wajen, kuma yayinda suke bincike, sai gashi ya fito daga cikin daji da jini a gaban goshinsa.

Mai idon shaidan ya bayyana cewa mutumin ya bayyanawa yan sanda cewa ya samu nasarar doke daya daga cikin yan bindigan ne kafin ya gudu daga mabuyarsu.

Ya ce yayinda ya fara gudu, daya daga cikin yan bindiga ya jefe shi da adda kuma ya ji masa rauni a gaban goshi, amma bai daina gudu ba har sai da ya tabbatar ya tsira.

Wata majiya a ma’aikatar ta tabbatar da aukuwan lamarin ga Daily Trust. Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, ya ce suna bincike kan lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here