Sabuwar Nau’in Cutar KoronaVirus ta Bayyana a Najeriya

Masana sun ce an fara samun masu dauke da kwayar SARS-CoV-2 a Najeriya.

Africa Centre of Excellence for Genomics of Infectious Diseases ta gano wannan.

Shugaban cibiyar binciken yace N501Y, A570D da HV 69 – 70 ba su bayyana ba.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto cewa sabuwar nau’in Coronavirus da yanzu haka ya ke tada hankalin al’umma ya bayyana a Najeriya.

Kwararrun masanan da ke aiki da cibiyar bincike kan cututtuka masu yaduwa a Afrika ta jami’ar Redeemers-Ede, Osun, su ka tabbatar da wannan.

Ana yi wa sabon nau’in COVID-19 wanda aka gano a Ingila a watan Satumba lakabi da lineage B.1.1.7.

A wani rubutu da masanan da ke aiki da wannan cibiya ta ACEGID su ka fitar a shafin Virological, sun yi ikirarin ganin cutar a jikin mutane a Osun.

Masanan sun ce sun fara ganin cutar ne a jihar Osun a jikin wani da aka dauki jininsa a Agusta.

A watan Oktoba, aka sake ganin da cutar a jikin wani. A dalilin barkewar cutar ne kasashen Duniya da-dama su ka sa takunkumin hana shiga Ingila, sannnan su ka hana mutanen yankin zuwa kasarsu.

Shugaban cibiyar bincike ta ACEGID, Farfesa Christian Happi wanda ya kware sosai a kan wannan harka ya ce sun ga B.1.1.7 lineage a Najeriya.

Duk da karuwar cutar COVID-19 da ake samu, Farfesan ya ce kawo yanzu 1% na masu jinya a Najeriya ne su ka kamu ta kwayar cutar SARS-CoV-2.

Masanin ya kuma bayyana cewa sauran nau’ukan COVID-19 irinsu N501Y, A570D, da HV 69 – 70, ba su kai ga bayyana a jikin mutanen kasar ba tukun.

Tun a jiya ku ka ji cewa sabuwar kwayar COVID-19 ta fara tsorata gwamnatin Najeriya, har an kai ga tunanin lafta takunkumi domin dakile yaduwar cutar.

Barkowar samfurin Coronavirus na SARS-CoV-2 ya sa kasashe sun daina zirga-zirga zuwa Ingila, inda irin wannan kwayar cuta ya fara bayyana kwanaki.

Gwamnatin Tarayya ta ce COVID-19 da ta dawo ta na da ban tsoro, dole a firgita da irin hadarinta.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here