Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Wani Jami’in Tsaro Tare da Garkuwa da Uwa da Danta

 

‘Yan bindiga sun sace wata mata da jaririnta a Garin Falgore a farkon makon nan.

An kashe wani mutumi daga cikin wadanda su kayi yunkurin kai wa iyalin dauki.

Miyagun sun shiga cikin karamar hukumar Rogo ne da tsakar dare a kan babura.

Wasu da ake zargin cewa ‘yan bindiga ne sun hallaka wani jami’in tsaron ‘dan-sa-kai a garin Falgore, karamar hukumar Rano, a jihar Kano.

Jaridar Premium Times tace ‘yan bindigan sun yi wannan ta’adi ne bayan sace wata mata da ke shayarwa, sun hada har da jaririnta, sun yi gaba.

Shugaban karamar hukumar Rogo, Malami Rogo, ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun shigo masu ne a tsakar daren ranar Lahadin nan da ta wuce.

Rogo ya ce ‘yan bindigan sun shiga gidan wani Alhaji Yusuf Falgore, su kayi wannan aika-aika.

Jami’an tsaro sun yi yunkurin ceto mutanen nan da aka sace, amma wadannan miyagu sun kashe guda daga cikin ‘yan sa-kan da su ka bi sawu.

Tuni aka yi wa mamacin sutura, aka birne shi yadda addini ya tanada, kamar yadda shugaban karamar hukumar na Rogo ya shaidawa ‘yan jarida.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Kano, Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari a garin mai iyaka tsakanin jihar Katsina da Kano.

Wani ma’aikacin BBC Hausa, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari, ya ce daga cikin wadanda aka kashe har da wani direban ‘yan sanda.

Mai taimakawa shugaban kasa wajen yada labarai, Femi Adesina yace rashin tsaro ya ragu a Najeriya domin yanzu bam sun daina tashi kamar lokacin baya.

Da ya ke magana a kan tsaro, Hadimin shugaban kasar ya ce an daina ruwan bam duk ranar Allah da zuwan shugaba Muhammadu Buhari kan mulki a 2015.

Fadar Shugaban kasar ta yi magana ne bayan an kai hari 5 a kwana 2 a wasu jihohin Arewa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here