Mutane Masu Hankali da Kuma Marubuta Tarihi ya Kamata su yi Adalci Akan Gwamnatina – Shugaba Buhari
Shugaban ƙasa Buhari ya yi kira ga marubuta tarihi a Najeriya da su yi wa gwamnatinsa adalci.
Shugaban yace gwamnatinsa ta fuskanci ƙalubale da dama tun lokacin da ta zo a shekarar 2015.
Buhari ya bayyana cewa farashin man fetur ya faɗi warwas a karkashin gwamnatin sa.
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi kira ga masana tarihi da masu hankali cewa su yi wa gwamnatinsa adalci wajen rubuta nasarorin da ta samu, kamar yadda the cable ta ruwaito.
A wani jawabi da Malam Garba Shehu ya fitar, Kakakin shugaban ƙasa, Buhari ya yi wannan kira ne yayin da ya karbi bakuncin wasu gwamnonin APC a mahaifarsa, Daura, jahar Katsina.
Buhari yace:
“Mutane masu hankali da kuma marubuta tarihi ya kamata su yi adalci akan mu. Waɗanda suke neman wani muƙami ba zasu gurbata abinda mutane suka gani a ƙasa ba.”
Read Also:
Mun yi namijin kokari Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi namijin kokari wajen ceto ƙasar nan idan aka kwatanta da yanda ƙasar take a 2015.
Yabe:
“Cigaban da aka samu a yankin arewa maso gabas abin jin dadi ne, domin a wancan lokacin mutanen dake rayuwa tare, suke magana da yare iri ɗaya, sune suka fara kashe junansu.”
“Idan kuka duba yanayin da gwamnatin mu ta tsinci ƙasar nan ta ɓangaren lokaci da kuɗaɗen shiga, zaku fahimci abubuwan da muka cimma wa.”
Farashin gangar mai ya faɗi.
Buhari ya ƙara da cewa daga zuwan gwamnatinsa farashin man fetur ya yi warwas a kasuwar duniya daga sama da dala $100 ya koma.
ƙasa da $38. Hakanan a wancan lokaci ana haƙo gangar ɗanyen mai miliyan 2.1m a rana ɗaya amma ya dauka zuwa ganga 500,000.
“Mun yi iyakacin kokarin mu, kuma mun gode Allah mun samu nasarori da dama, in banda haka da yanzun mun shiga matsala,” inji Buhari.