Adamawa: Duk Wanda Bai Dawo da Kayan da ya Sata ba za a Rushe Gidansa – Gwamnan Jahar

 

  Gwamnan Jihar Adamawa ya bai wa waɗanda suka sace kayayyakin abinci a jihar wa’adin awa 12 da su mayar da abin da suka sata ko kuma a rushe inda suka ɓoye su.

  Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya bayyana haka ne a yau Talata cikin wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar.

  “Na ba da wa’adin awa 12 daga 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe ga ‘yan dabar da su dawo da dukkanin abin da suka sata daga ma’adanin gwamnati da na mutane ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su,” in ji gwamnan.

  “Wannan wa’adin zai ƙare da 6:00 na safiyar Laraba, 28 ga Oktoba, wanda bayan haka zan bayar da umarnin shiga gida-gida domin bincike da ƙarfe 7:00 na safiyar.

  “Ɗaya daga cikin umarnin shi ne ƙwace shaidar mallaka ko kuma rushe gidan da aka ɓoye kowane irin kayan da aka sata. Ya kamata ‘yan ƙasa na gari su bai wa jami’an tsaro haɗin kai don ganin an tabbatar da dokar.”

  Haka nan Gwamna Fintiri ya ce dokar hana fita ta awa 24 da aka saka a jihar “ta zama dole ne” bayan tuntuɓar hukumomin tsaro domin “daƙile ayyukan ‘yan daba”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here