Abuja: Hukumar NSCDC ta Sallami Hafsan da Aka Gani a Bidiyo Yana Wawason Kayan Abinci

 

Jami’in NSCDC ya rasa aikinsa sakamakon satan kayan abincin COVID-19 a Abuja

A ranar Litinin bata gari suka fasa runbun abinci a unguwar Gwagwalada sukayi wawason kayan hatsi

Wasu sun dauki bidiyon hafsan NSCDC yana dauka nasa rabon Hukumar tsaron farin hula watau Sibil Defens ta sallami wani hafsan ta, Iliya Ibrahim, daga aikin bayan bayyanar bidiyon dake nuna shi ya saci kayan abinci yayinda matasa suka fasa rumbun abincin tallafin Korona a unguwar Gwagwalada Abuja.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an ga Iliya Ibrahim sanye da kayan sarki ya debi wasu kayan abinci lokacin da matasa ke wawaso. Sallamar Ibrahim na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun shugaban hukumar, Ekunola Gbenga, ya sake ranar Talata.

Wani sashen jawabin yace: “Kwamanda Janar, Abdullahi Gana Muhammadu ya amince shawarar kwamitin ladabtar da kananan hafsoshi na sallamar Iliya Ibrahim na Gwagwalada kan hada kai da matasa wajen satan kayan tallafin COVID-19 a wani runbun abinci.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here