Barcelona: Bartomeu ya yi Murabus a Mastsayin Shugaban Kungiyar

Joseph Bartomeu ya bata wa kansa suna bayan rikicin da ya yi da Lionel Messi a watannin d suka gabata.

Tauraron na Barcelona Lionel Messi da farko ya mika wa kungiyar wasikar neman tafiya amma daga bisani ya canja ra’ayinsa

Shugaban kungiyar Josep Bartomeu ya yi murabus tun kafin ayi masa kuri’ar rashin amincewa a kore shi Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Maria Bartomeu ya yi murabus a ranar Talata 27 ga watan Oktoba kafin a jefa kuri’ar rashin amincewa a kansa kafin a kore shi kamar yadda SunsSport ta ruwaito.

An kuma gano cewa wasu direktocin kungiyarda dama suma sun yi murabus daga matsayinsu.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kungiyar ta Barcelona ta sha kaye 3-1 a hannun abokan hammayarsu na gida Real Madrid a El Classico ta farko na wannan kakan wasar.

Sunan Bartomeu ta baci ne bayan yadda ta kaya tsakaninsa da fitaccen dan wasan kungiyar Lionel Messi wadda da farko ya mika wasikarsa ta neman barin kungiyar. Ya ki canja ra’ayinsa wadda hakan ya kusa saka fitaccen dan wasan da ya lashe Ballpn d’Or guda shida barin kungiyar bayan shekaru 20

Magoya bayan kungiyar wadda sune suka mallakikungiyar sun yi taro sun kuma samu adadin sa hannu da ake bukata don fara yi jefa masa kuri’an rashin amincewa. Idan ba a manta ba tunda farko da Messi ya yi barazanar barin kungiyar, mahaifinsa Jorge ya shiga jirgi ya zo Barcelona amma ba su daidaita ba. Kuma duk da kullen korona da aka saka a kasar, magoya bayan kungiyar sun yi tururuwa zuwa Camp Nou inda suka bukaci Bartomeu ya yi murabus. Hakan ne ya janyo suka fara shirin tattara kuri’u don jefa zaben rashin amincewa da shi. An zargi Bartomeu da rashawa a watan Satumba yanzu ya yanke shawarar yin murabus kafin a kore shi

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here