LABARI DA DUMI-DUMINSA: Legas ta Sake Rikicewa #ENDSARS

An lalata motocin BRT da dama a Lagos ranar Talata, 27 Oktoban shekarar 2020 – Yan tawayen sun aikata barnar tasu a Mil 2 wani bangare na jahar ta Legas

Rahotanni sun bayyana cewa a fasa shaguna da kantina da dama a yankin Ga dukkan alamu yan tawaye a Legas basu gama da lalata kayayyaki ba inda suka waiwayi yankin Mil 2 suka kuma ci gaba da barna a ranar Talata 27 ga Oktoba a yankin da ke jihar Legas.

A wani rahoto mai ban tsoro da PM News ta fitar ya nuna cewa wasu gungun ‘yan daban sun lalata da yawa daga cikin motocin BRT kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

An kuma hango su da adduna suna fashe shaguna a yankin inda rikicin ya barke har Owade axis kan hanyar Ikorudu. Wannan ya tilasta Primero, mai kula da motocin BRT fara tunanin dakatar da da al’amura saboda gudun kada a ci gaba da lalata musu motoci.

Sai dai kuma, wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa yan jarida cewa tuni aka girke jami’an yan sanda a yankin don saita al’amura da dawo da zaman lafiya.

A makamancin hakan, wasu fusatattun matasa sun sauke fushinsu akan gwamnan jihar, Babajide Sanwa-Olu. Matasan kamar yadda jaridar This Day ta rawaito, sun cinna wa gidan mahaifiyar Sanwa-Olu wuta ranar Laraba 21 ga Oktoban 2020.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here