Kotu ta Umarci Atiku Abubakar da ya Mayar da Tsohuwar Matarsa

Babbar kotun Kubwa da ke birnin Abuja, ta umarci Abubakar Atiku da yayi gaggawar mayar wa tsohuwar matarsa yaransu 3

Abubakar Atiku, da ne ga tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, dama ya kwace yaran 3 ne tun bayan rabuwarsu

Alkali Mai shari’a, Bashir Danmaisule, ya ce Abubakar bai gabatar da hujjojin da za su hana Maryam Sherif rike yaranta ba Wata babbar kotu da ke Kubwa a Abuja, ta umarci Alhaji Atiku Abubakar da ya mayar wa Maryam Sherif,

tsohuwar matarsa yaransu 3 da ke hannunsa take-yanke. A shekarar da ta gabata ne Maryam ta maka Abubakar kotu, inda take bukatar ya bata yaransu maza 3 da yake rike dasu. Abubakar da ne ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Alkalin kotun, Bashir Danmaisule, ya ce Abubakar bai bayar da wata hajja a musulunce da za ta hana uwar amsar yaranta ba. Amma zai iya daukaka kara cikin kwanaki 30.

A kotun, Maryam da lauyanta, Nasir Sa’idu sun halarci zaman, yayin da Abubakar da lauyansa , Abdullahi Hassan kuwa basu je ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here