Shugaban Majalisar dokoki: An Dauke Wasu Mutane 2 Daga Gidan
An auka gidan Shugaban Majalisar dokokin Adamawa an yi barna a jiya.
‘Yan Sanda sun tabbatar da cewa an kashe wani Mai gadi 1 da aka samu .
‘Yan bindigan sun tsere da mutane biyu da aka samu a gidan Iya-Abass Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu ‘yan bindiga da ba a sansu ba sun auka gidan shugaban majalisar dokokin Adamawa, Aminu Iya-Abass, sun yi ta’adi.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun sace wasu mutane biyu daga cikin iyalin Rt. Hon. Aminu Iya-Abass a gidansa da ke Mbamba, a jihar Adamawa.
Kamar yadda jaridar ta fahimta, wadannan miyagu sun auka gidan ‘dan siyasar ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba, 2020, su ka kashe mutum guda.
Read Also:
Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da wannan hari a ranar Juma’a, amma sun karyata rahotannin da ke yawo na cewa an kashe wani ‘dan sanda a harin na jiya, Majiyar jami’an tsaron ta ce: “A harin, ‘yan bindigan sun kashe wani daga cikin ‘dan banga da ke gadin gidan, yayin da wani jami’in ‘dan sanda ya samu rauni.”
Kakakin ‘yan sanda na jihar Adamawa, Suleiman Nguroje, ya ce ‘yan bindigan sun tsere da wasu mutane.
“A jiya (Alhamis), ‘yan bindiga sun kai hari a wani gida, su ka kashe ‘dan kato-da-gora, kuma su ka tsere da mutum biyu daga gidan.” Inji Suleiman Nguroje.
ami’an tsaro sun je gidan da karfe 4:00 na safe, su ka yi kokarin kawo dauki, amma sun makara.
Nguroje ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa, Olugbenga Adeyanju, ya bada umarnin ayi maza a gano wadanda su ka yi wannan mummunan aiki.