Obasanjo: Dalilin da Yasa Aka Tsige Rashidi Ladoja Daga Gwamna a Shekarar 2006

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi waiwaye adon tafiya a kan dalilin tsige tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja.

Ladoja ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Oyo a shekarar 2003 amma sai aka tsige shi kafin ya kammal wa’adinsa na farko.

An samu mabanbantan rahotanni a kan dalilin tsige Ladoja a wancan lokacin Tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana babban dalilin da yasa aka tsige tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja.

Obasanjo ya bayyana hakan ne lokacin taron gabatar da littafin tarihin Adebayo Alao-Akala, wani tsohon gwamnan jihar Oyo.

A cewar Obasanjo, an tsige Ladoja ne sakamakon rashin ɗa’a ga Marigayi Lamiidi Adedibu, ubangidan siyasar jihar Oyo, da kuma Yekinni Adeoja (mashahurin ɗan siyasa a jihar).

Obasanjo wanda yace ya gano cewa Ladoja ya fara rigima da shi a littafin tarihin Alao-Akala inda yace Ladoja ya biya maƙudan kuɗaɗe don a ɓoye aibunsa.

“Ka rubuta a shafi na 140 cewar Ladoja ya fara rigima da ni sakamakon rashin bani goyon baya domin yin tazarce a karo na uku, wanda babu shi a tsarin doka,” a cewarsa

“Ban san cewa Ladoja yana rigima dani ba, kuma dalilin zamansa gwamna albarkacin gudunmawar da ya samu ne daga mutane biyu; wato Lamidi Adedibu da Yekenni Adeojo.

“Na roƙe shi akan ya basu matsuguni gaba ɗayansu, amma sai yace min dukkansu mutanen Ibadan ne don haka su san inda zasu sa kansu.

“Ta tabbata cewa ya yi dai-dai domin kuwa sun san inda suka yi da kan nasu.

Sai dai kuma sakamakon haka al’amura sun kwaɓewa Ladoja, don kuwa ya kwana ciki.

” A lokacin, Alao-Akala shine mataimakin gwamnan jihar Oyo, daga shekarar 2003-2007, kafin daga bisani ya maye gurbin Ladoja bayan an tsige shi daga kujerar gwamna

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here