Adamawa: Wani Yankin Jahar na Fuskantar Kangin Rayuwa

 

Da rashin muhimman gine-gine masu amfani, Folwoya Goriji, wani gari a jihar Adamawa, na fuskantar kangin rayuwa.

A garin babu tsaftataccen ruwan sha wanda hakan yasa mazauna garin ke shan ruwa a kogi daya da dabbobinsu.

Mazauna yankin, yayinda suke korafi, sun bukaci a kawo masu dauki saboda suna tunanin an manta da su.

Folwoya Goriji, wani garin manoma a yankin Ndikong da ke karamar hukumar Mayo Belwa na jihar Adamawa, na da hanyar samun ruwa guda daya ne tal.Abun bakin ciki, a wuri guda mutane da dabbobi ke samun ruwan sha.

A cewar The Pilot, wannan garin sun dogara ne a kan ruwan kogo wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullun, sannan sun yarda cewa wakilan jiharsu da na hukumarsu sun watsar da su.

Al’umman kauyen na rokon gwamnatocin jiha da na kananan hukumomi su share masu hawayensu daga illar da ke tattare da shan ruwa a waje guda da dabbobinsu.

An kawo Baba Musa, wani mazaunin kauyen, ya na fadin cewa:

“A lokacin yakin neman zabe ne kawai muke ganinsu (yan siyasa) tare da alkawaransu na bogi da karya. Don Allah, kalli ruwan da muke sha tare da dabbobinmu kamar an manta da mu.

“Dan Allah ku fada masu kokenmu,” yan asalin garin.”

Da yake martani ga koken Musa, wani mai kare hakkin dan adam, Ibrahim Makejo, ya bayyana cewa ba garin kadai bane domin akwai saura da ke fuskantar irin wannan wahala ta rayuwa.

“Ruwan sha mai inganci, gyara da tsafta na daga cikin hanyoyi biyar na dakile cututtuka.

“Saboda haka yana da muhimmanci zababbun shugabanninmu su samar da ruwa mai inganci, da tabbatar da tsaftar muhalli da na jiki a yankunan karkara.

Legit.ng ta yi kokarin samun kansila da ke wakiltan yankin amma abun ya ci tura domin an ce baya gari.

Yunkurin jin ta bakin Shugaban karamar hukumar ma bai haifar da yaya masu idanu ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here