Addinin Musulunci Addini ne Mai Samar da Zaman Lafiya – Gwamnan Kano ga Malamai

Gwamnan jahar Kano ya gargadi malamai da su daina yin wa’azin da zai ke tada hankali.

Gwamnan ya bayyana cewa addinin musulunci addini ne mai Samar da zaman lafiya.

Ya kuma siffanta da’awar Annabi Muhammadu (S.A.W) da da’awar zaman lafiya.

da son juna Gwamna Abdullahi Ganduje na jahar Kano ya gargadi malaman addinin Islama da su daina yin kalamai masu tayar da hankali, wadanda za su iya keta zaman lafiya, yayin wa’azi, The Guardian ta ruwaito.

Ganduje ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a Kano lokacin da ya gana da Limamai na Masallacin Juma’at da sauran malaman addinin Musulunci a jahar.

Ya tunatar da malamai matsayinsu a cikin al’umma, yana mai cewa ya kamata su yi iya kokarinsu ko yaushe su zama abin koyi na fatar baki ko a aikace.

Ya kuma yi kira ga limamai su fito da hanyoyin da za su yada koyarwar addini na hakika.

“Annabi Muhammad ya yi wa’azin zaman lafiya, soyayya da hadin kai kuma a matsayinmu na mabiya addinin Musulunci na gaskiya, ya kamata mu yi koyi da irin wannan domin mu more rayuwa anan da kuma har abada,” in ji shi.

Gwamnan ya bukaci ‘yan Najeriya su yi hakuri da juna, su zauna lafiya da juna, ba tare da la’akari da bambancin addini, al’adu da kabilanci ba.

Wata sanarwa da gwamnatin ta bayar ta umarci dukkan tashoshin watsa shirye-shirye da dandalin sada zumunta da su daina yada wa’azi, wa’azozi da duk wata tattaunawa ta addini da ka iya haifar da rashin zaman lafiya a jahar.

Ta kuma umarci hukumomin tsaro da su tabbatar sun cika ka’ida tare da daukar kwararan matakai kan mutanen da suka yi kuskure ko kuma kungiyoyin da aka samu suna bijirewa umarnin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here