Wutar Lantarki: Bankin Duniya Ya Taimakawa Najeriya da Kudi $500m

 

Bankin Duniya ta baiwa Najeriya wani tallafi mai muhimmanci ga al’umma.

Najeriya na cikin kasashe mafi fama da rashin wutan lantarki a duniya, cewar bankin duniya.

Kusan rabin yan Najeriya basu gani hasken wutan lantarki gaba daya.

Bankin duniya (World Bank) ta taimakawa Najeriya da kudi $500m don inganta wutan lantarki da kuma karfafa kamfanonin raba wutan lantarki a kasar.

A jawabin da bankin ta saki ranar Juma’a, za ta baiwa kamfanonin dake raba lantarki da sharadin sun cimma manufar inganta wutan lantarki da mutane.

Jawabin yace, “Yan Najeriya milyan 85 ba su da wutan lantarki. Hakan na nufin cewa kashi 43% na jama’ar kasar kuma Najeriya ce kasar dake gaba wajen rashin isasshen wutan lantarki.”

“Rashin lantarki babban kalubalee ne ga al’umma da kasuwancinsu, kuma hakan na sabbasa hasarar kimanin $26.2 billion (₦10.1 trillion).”

“Bisa rahoton saukin kasuwanci da World Banka ta saki a 2020, Najeriya ce kasa ta 171 cikin kasashe 190 da ake ganin rashin lantarki ne babban kalubale ga kamfanonin masu zaman kansu.”

Jawabin ya nakalto Diraktan World Bank na Najeriya, Shubham Chaudhuri da cewa, “Inganta wutan lantarki na da muhimmanci wajen rage talauci da inganta tattalin arziki bayan annobar COVID-19.”

Hadimin Buhari, Tolu Ogunlesi, ya tabbatar da wannan labari a jawabin da yayi a shafinsa na Tuwita.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here