Covid-19: Prince Samuel Adedoyin ya Rasa ‘Yarsa, Lola Olabayo
Prince Samuel Adedoyin, wani hamshakin dan kasuwa ne dan asalin jahar Kwara, ya rasa diyarsa, Princess Lola Olabayo ranar Talata.
Mummunan lamarin ya faru ne bayan wata biyu da Subomi, dan sa ya halaka kansa, duk da dai ba a san kwakkwaran dalilinsa na yin hakan ba.
Rahotanni sun tabbatar da yadda ta kwashe kwana bakwai a asibitin jahar Legas tana fama da cutar sarkewar numfashi ta COVID-19.
Kwara – Prince Samuel Adedoyin, wani hamshakin biloniya dan asalin jahar Kwara ya rasa diyarsa, Princess Lola Olabayo.
Mummunan lamarin ya faru ne yana tsaka da jimamin mutuwar dansa Subomi da watanni biyu bayan ya yi ajalin kansa, duk da dai ba asan dalilinsa nayin hakan ba.
Read Also:
An samu labarin yadda ta rasu a asibitin jahar Legas bayan kwashe kwana 7 kwance sakamakon fama da cutar COVID-19.
Sai dai wata majiya daga iyalinsa wacce bat bukaci a bayyana sunanta ba, ta musanta cewa cutar ce ta kashe ta.
Mahaifin mamaciyar ya tabbatar da mutuwarta inda yace za su sanar da ranar da za a yi bikin birneta.
A cewarsa:
Ta rasu a ranar Talata da daddare a asibitin Legas. Za mu yi taron mu na ‘yan uwa don a tattaunawa akan ranar da za a tsayar don a yi bikin birne ta.
Za mu saki takarda bayan mun kammala taron, a cewar mahaifin mamaciyar.
Bayan wakilin Daily Trust ya kai ziyarta gifan Olobayo dake GRA a ranar Laraba, ya taras babu mutane sosai.
Funke, daya ce daga yaran Adedoyin kuma ta rasu ne a 2018.
Ta rasu ne lokacin tana rike da kujerar ‘yar majalisar wakilai bayan tayi fama da cutar daji.