EU za ta Fara Aika Makamai Zuwa Ukraine
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta European Union (EU) ta sanar da cewa za ta fara aika makamai zuwa Ukraine.
Wannan ne karon farko da EU za ta yi hakan a tarihinta.
Read Also:
Da take magana yayin taron manema labarai a yammacin nan, Shugabar Hukumar Turai Ursula von der Leyen ta ce yunƙurin na nufin “samun sauyi”.
Ta kuma sanar da wasu jerin takunkumai da aka saka wa Rasha da Belarus, ciki har da hana jiragen ƙasar bi ta sararin samaniyar ƙasashen ƙungiyar.