Ku Aikata Wadannan Abubuwan Idan Sun Caka Muku Makami
1-Idan sun caka kuma sun zare a ko wanne ‘bangare ne a jikin bil’adama. Toh, ya zama wajibi ku yi gaggawar samun wani abu mai tsafta ku danne wajan domin sa pressure wacce za ta rage zubar jini.
2-Sannan ku tabbata ba ku tsaya ta kwato waya ba, domin yin hakan zai cutar da wanda aka sokawa makamin. Saboda yawan zubar jinin zai iya hulla shi ya fita daga hayyacinsa, ya fada abun da muke kira da Shock. Zuwan asibiti da wuri (Early Presentation) yana taka rawar gani wajan ceto rayuwa.
3-Ya zama wajibi kar ku dinga jagwalgwala wanda aka sokawa, da inda aka soka makamin. Ku tabbata kun kwantar dashi yadda ba zai takura ba, a kwantar da shi ta ‘bangaren sa na hagu (Wato Left Lateral Position). Yin hakan na taimakawa zuciya ta tunkud’o jini da sauran ayyuka yadda ya kamata.
Read Also:
4-Idan kuma sun caka sannan sun bar makami a jiki; Dan girman Allah kada ku yi yunkirin cirewa! Domin cirewa, zai iya salwantar da rayuwa ta ‘ballewar jini ya yi ta zuba. Abun da za ku yi shine ku nad’e gefe da gefen inda makamin yake wato kusa pressure. Sannan kada ku bari shima ya yi yunkurin cirewa da kanshi ko da ba ya jin dadi.
5-Idan san samu ne ku tanadi wadanda za su iya bada gudunmawar jini tun kuna kan hanyar zuwa asibiti. Yin hakan zai iya rage jan jiki wajan saka jini idan likitoci sun tabbatar da bukatuwar hakan.
6-Dan Allah kada ku cika gaban likita da jama’a. Domin ana bukatar nutsuwa, iska, da yanayi mai kyau duk don ceto rayuwar mara lafiyar da ku ka kawo gaban “Likita”.
Mu Sani Cewe:
Jama’a da yawa sun rasu domin rashin yin wadannan abubuwa dana zayyana a sama. Ina mai tabbatar muku cewa idan akai amfani da wad’annan shawarwari salwantar rayukan zai ragu insha’Allah.
Kullum dai “Rigakafi Ya Fi Magani”.
Bissalam!
Dr Khalid Sunusi Kani
Likita Kuma Mai Wayar Da Al’umma Akan Cututtuka Da Dama.