Tabbas Ma’aikatan Lafiya Sun San Rashin Imanin ‘Yan Kwacen Waya

 

Duk Wanda Ke Aiki a ‘Dakin Taimakon Gaggawa (Accident And Emergency) Zai Tabbatar Maka Cewa ‘Yan Kwacen Waya Ba Su Da Imani. Domin Ganin Yadda Yaran Su Ka Gama Nazartar Duk Wata Makasar Bil’adama a Jikin Sa. Kama Daga Kai Har Zuwa ‘Kafa. Wannan Abun Tashin Hankali Ne Tabbas!

Ha’ki’ka Mun Gaji Da Ganin Rashin Imanin Yarannan! Ya Zama Wajibi Mahukunta Su ‘Dauki Mataki.

Gargadi!

Duk Sadda Marasa Mutumcin Yarannan Suka Sokawa Wani Makami a Cikin ‘Kirji Ko Ciki, Kuma Suka Gudu Ba Tare Da Zare Wannan Makami Ba. Toh, Kada Ku Yi Karanbanin Cirewa Mutum Da Kanku. Domin Yin Hakan Na Da Illa. Zai Iya Kawo Salwantar Rayuwa, Irin Wannan Ciyo Muna Kiranshi Da “Impalement Injury” Mu Likitoci Kadai Ne Mu Kasan Yadda Za Mu Yi Da Wannan Abu.

Shin Ina Ki/Ka Fi Ganin Yarannan Sun Fi Cakawa Mutane Makami a Jiki?

Insha’Allah Zanyi Bayani Dalla-Dalla Kan Yadda Za Ku Ba Da Taimakon Gaggawa Idan Wannan Ibtila’i Ya Sami Wani a Gaban Ku.”

Dr. Khalid Sunusi Kani
Likita Kuma Mai Wayar Dakan Al’umma Kan Cututtuka Da Dama.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here