Gidauniyar AMG ta Ɗau Nauyin Karatun Gwarzuwar Alqur’ani, Aisha Abubakar har ta Gama Jami’a

 

Daga Hannatu Sulaiman Abba

AREWA AGENDA – Gidauniyar Aminu Magashi Garba ta ɗau nauyin karatun Aisha Abubakar wanda ta zo ta biyu a gasar karatun Al’kur’ani da akayi a kasar Dubai a shekarar da ta gabata.

Wakilin Gidauniyar Malam Suleiman Jalo ne ya bayyana Haka, inda ya ce tun farkon samu labarin irin kokarin da Aisha tayi, yasa shugaban Gidauniyar Dakta Aminu ya umarci a fara binciko hafiza tare da tallafawa karatun ta.

Hakazalika, Gidauniyar ta yi kokari wajen sama Mata gurbin karatu a jami’ar Yusuf Maitama Sule dake Jahar Kano, inda zata karanci fannin ‘Kemistari’ tsahon shekara 4.

Gidauniyar Aminu Magashi Garba dai ta biya kudin litattafai tare da daukar alkawarin bata naira Dubu Goma a duk wata domin jigilar kudin mota.

Ba wannan ne karon farko da Gidauniyar ta fara daukar nauyin dalibai ba tare da taimakon al’umma domin cigaba me dorewa a jahar Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here