Jihata na Daga Cikin Jihohin da Ma’aikata ke Samun Albashi a Kan Kari – Gwamna Buni

 

Gwamnan jihar Yobe ya bayyana cewa, jiharsa na daga cikin jihohin da ma’aikata ke samun albashi a kan kari.

A baya wani rahoto ya shaida cewa, akwai wasu jihohi da dama a kasar nan da ke fama da rashin biyan ma’aikata albashi a kan kari.

Baya ga batun biya a kan lokaci, karancin albashi na daya daga cikin abubuwan da ma’aikata a Najeriya ke fama dashi duba da tattalin arzikin kasarsa.

Jihar Yobe – Gwamna Mai Mala Buni na Yobe a ranar Juma’a ya ce gwamnatinsa na kokari wajen biyan albashin ma’aikata duk da karancin kudi da jihar ke da shi, Guardian ta ruwaito.

Buni, a wata sanarwa da babban daraktan yada labaran sa, Mamman Mohammed, ya fitar a Damaturu, ya ce wani bincike da wata kafar fasaha ta BudgIT ta gudanar ya tabbatar da hakan.

A cewar gwamna Buni:

“Rahoton binciken wanda ya tsaya a Yuli 2022, ya nuna jihar Yobe a matsayin daya daga cikin jihohin da ma’aikatan gwamnati ba sa bi bashin albashi.”

Gwamnan ya bada tabbacin cewa biyan albashin ma’aikatan gwamnati a kan kari zai ci gaba da zama babban abin da gwamnatinsa ta sa a gaba, rahoton Independent.

A kalamansa:

“Duk da karancin kudi da jihar ke da shi, wannan gwamnatin ta jajirce kuma ta tsaya tsayin daka wajen biyan albashin ma’aikata, kuma za ta ci gaba da hakan.”

Buni ya kara da cewa:

“Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa ba za mu taba kasawa wajen biyan albashin ma’aikatanmu ba.”

Sai dai ya bukaci ma’aikatan da ke cin albashi na jiha da na kananan hukumomi da su mayar da hankali a kan ayyukansu ta hanyar aiki tukuru, sadaukarwa da kuma jajircewa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya bayyana cewa, a baya Budget, a 2020 ta sanya jihar Yobe ta biyu cikin jihohi mafi kyawun sarrafa kudi a kasafin kudin kasar.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here