Shirin Humanitarian Open House: Yadda Ma’aikatar ta Baiwa Dubban Mutane Mamaki Dangane da Aiyukan da ta Cimma
A ranar 22 ga Maris, 2022 ne dubban ‘yan Najeriya suka rasa abin faɗa game da ayyukan Ma’aikatar kula da harkokin jin kai, Agaji da inganta rayuwar al’umma.
Ya zama sanannen abu ga ‘yan Najeriya irin gagarumin ƙoƙarin da ma’aikatar ke yi na inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Duk wani shakku game da ayyukan da ma’aikatar ke yi ya gushe, a gun ‘yan Najeriya da ma waɗanda ba yan ƙasar ba, sun samu damar shiga cikin shirye-shiryen ma’aikatar, ayyuka, matakai da nasarorin da ma’aikatar ta samu.
Don haka da yawa daga cikin maganganun shakku ya haifar da zarge-zarge da labaran karya a tsakanin yan adawa, maganganu na yawo a fadin kasar akan ayyukan da ma’aikatar ke yi, da kuma dalilin da yasa ma gwamnati mai ci ta ƙirƙiro ma’aikatar, amma kuma gaskiya bata boyuwa.
Shirin Humanitarian open House, ya baiwa ‘yan Najeriya damar ganin hakikanin abin da ma’aikatar ke yi, da kuma samun damar yin tambayoyi game da kowace hukuma da shirye-shiryenta.
Mahalarta taron sun yi mamaki matuka ganin zahirin yadda, aka baje kolin yadda ‘yan Najeriya ke cin gajiyar shirye-shiryen wannan gwamnatin mai ci, karkashin kulawar ma’aikatar jin kai, agaji da inganta rayuwar al’umma.
A bayyane kamar na Sashen Ma’aikatar, daban-daban na shirye-shirye a karkashin National Social Investment Programmes, Hukumomin ma’aikatar da sauran masu ruwa da tsaki da abokan hulda sun ba da dukkan bayanan da ake bukata dangane da ayyukan jin kai, da ayyukan kare al’umma da ke gudana a kasar.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bayyana kayayyakin aikin su da motocin da ake amfani da su wajen ceton rayuka a duk lokacin da annoba ya afku.
Read Also:
Waɗanda suka ci gajiyar shirin National social investment program, daga jahohi daban-daban sun zo don bayyana ra’ayoyin su dangane da amfanin da shirin ya musu, da bada shaidar yadda tasirin shirin ya inganta ga rayuwarsu.
Ina iya tuna lokacin da nake kallon shirin a talabijin, lokacin da wasu mutane biyu waɗanda sun ci gajiyar shirin na Npower suka shaida wa kowa yadda shirin ya taimake su suka zama masu dogaro da kai, da kuma zama yan kasuwa, bayan wani mawuyacin yanayin da suka shiga a rayuwa a baya.
Mutanen da ke fama da nakasa ma ba’a bar su a baya ba. Wasu daga cikin nakasassun, sun samu damar halartar taron, sun kuma ba da shaidar abubuwan da ma’aikatar tayi musu na inganta rayuwar su.
Ma’aikatar ta kaddamar da manufofi, ga ‘yan gudun hijira a wurin taron.
A lokacin da wani daka cikin abokai na ya kirani a waya, ya ce min na kunna talabijin, da fari na ɗan samu shakku, daga karshe nayi farin ciki matuka a yayin dana fara kallo. Ba wai akan cibiyar ma’aikatar agajin ko shedar da masu cin gajiyar shirin ke bayarwa bane, face irin yanayin da ma’aikatar ke bayyana ayyukan da ta ke yi a zahiri wa al’umma don su gani, abokan adawa ma a wannan karon sunyi shiru ganin yadda ma’aikatar kula da harkokin jin kai, agajin da inganta rayuwar al’umma, ta samar da tarihi saboda, akaron farko a tarihi ma’aikatar ta samar da wani shiri, shirin (Open House) wanda yake baiwa al’ummar kasar damar yin tambayoyi game da aikin da ake yi da samun karin bayani, dama bada shawarwari.
Duk da manyan baki da suka halarci taron, ba a hana kowa shiga zauren taron ba, Lallai idan har wasu ma’aikatu za su yi koyi da FMHADMSD, Nigeria za ta zama kasar da muke mafarkin ta zama.
Na fahimci cewa ba batun siyasa ba ne, batu ne na waye a shirye da zai yi wa ’yan Najeriya aiki, kuma a yau kamar yadda nakasassu suka fada a wajen taron, a matsayinq na ɗan Najeriya kuma mai kishin ƙasa, ina cewa na gode Sadiya Umar Farouq.