Kasar Aljeriya ta yi Rashin Tsofaffin Shugabanninta 2
A cikin mako guda, Aljeriya ta rasa tsohon shugabanninta biyu, Abdelkader Bensalah da Abdelaziz Bouteflika.
Yayin da Bensalah ya rasu a ranar Laraba, 22 ga watan Satumba, Bouteflika ya mutu a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba.
A dunkule, tsofaffin shugabannin biyu sun kasance a mulki sama da shekaru ashirin kafin shugaban kasar na yanzu, Shugaba Abdelmadjid, ya hau karagar mulki.
Aljeriya – Abdelkader Bensalah, tsohon shugaban rikon kwarya na Aljeriya wanda ya jagoranci kasar ta Afirka a shekarar 2019 lokacin da take fama da mummunan rikicin kasa, ya mutu.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a cewar fadar shugaban kasar Aljeriya, Bensalah ya rasu a ranar Laraba, 22 ga watan Satumba, yana da shekaru 80.
Read Also:
Bensalah, wanda ya kuma shugabanci majalisar dattijai ta Aljeriya na tsawon shekaru, ya ci gaba da mulki har zuwa lokacin da aka zabi Shugaba Abdelmadjid Tebboune a karshen shekarar 2019.
An tattaro cewa rasuwar Bensalah ta zo ne bayan doguwar gwagwarmaya da wata cuta da har yanzu ba a bayyana sunan ta ba.
Ana sa ran za a yi jana’izar marigayi shugaban kasar bayan addu’o’i a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba, a makabartar El Alia, gabas da tsakiyar Algiers.
Mutuwar Bensalah ta zo ne kasa da kwanaki bakwai bayan da aka ayyana mutuwar wanda ya gada, Abdelaziz Bouteflika, a ranar Juma’a, 17 ga watan Satumba.
Bouteflika ya mutu shekaru biyu bayan ya sauka daga mukaminsa bayan zanga -zangar da talakawa da sojoji suka yi a fadin kasar bayan labarin shirinsa na tsayawa takara a wa’adi na biyar ya bayyana.
Ya ci gaba da rike madafun iko a cikin kasar na akalla shekaru 20 kafin daga bisani ya yi murabus a shekarar 2019 bayan korafe -korafen jama’a da dama daga ‘yan kasar wadanda suka gan shi a matsayin mai mulkin kama -karya.
Bayan Bouteflika ya bar ofis, da kyar ake ganin shi a bainar jama’a har zuwa rasuwarsa a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba.