2023: Jahohi 24 da Farfesa Attahiru Jega Zai Soke Idan ya Zama Shugaban Kasa

 

Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ya yi imanin cewa hanya guda da zai bi wajen kawo canjin da ake so a Najeriya shi ne shiga siyasa da kuma yiwuwar shiga takarar shugaban kasa a 2023.

Ana kyautata zaton Jega zai tsaya takara a jam’iyyar Rescue Nigeria Project (RNP) tare da wasu manyan masu sharhi kan al’amuran yau da kullum kamar Pat Utomi da Donald Duke, tsohon gwamnan Kuros Riba.

Jega na da ra’ayin cewa rushe tsarin jahohi 36, da sake daidaita jahohin zuwa yankunan siyasa na kafin shekarar 1966, ko ma zuwa jahohi 12 na zamanin 1976/77 yana daya daga cikin mafi dacewa a hanyoyin fitar da ci gaba cikin sauri a fadin kasar nan.

A yayin taron farko na kungiyar RNP a Abuja a ranar Litinin, 20 ga Satumba, Jega ya lura cewa magangan da ake a yanzu na kirkirar wasu jahohi wani yanki ne na nuna wariya a wasu yankuna.

A cikin shawararsa, Jega ya ba da shawarar cewa soke wasu jahohi, akalla 24 daga cikin su, za su kasance abu mai yiwuwa da fa’ida.

Daily Trust ta rawaito shi inda yake kushe yunkurin da wasu ke yi na taso da maganar kara jahohi a Najeriya su kai 42.

Jerin jahohin da za a soke su a Najeriya

Idan RNP ta ci nasarar karbe ragamar Najeriya, a kasa ga jerin jahohin da za a soke su daga 2023.

1. Abia

2. Adamawa

3. Akwa Ibom

4. Anambra

5. Bayelsa

6. Borno

7. Delta

8. Ebonyi

9. Edo

10. Ekiti

11. Enugu

12. Gombe

13. Jigawa

14. Katsina

15. Kebbi

16. Nasarawa

17. Ogun

18. Ondo

19. Osun

20. Oyo

21. Sokoto

22. Taraba

23. Yobe

24. Zamfara

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here