Minista Sadiya Farouq ta yi Allah Wadai da Harin da Aka Kai wa Garuruwa Biyar a Jahar Plateau

Ministar kula da harkokin jin kai, agaji da inganta rayuwar al’umma, Sadiya Umar Farouq ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a wasu garuruwa biyar a jihar Filato inda ta bayyana hakan a matsayin shaiɗanci.

Sadiya Umar Farouq ta jajantawa gwamnatin jihar da waɗanda harin ‘yan fashi da makamin ta rutsa da su, a Garga da ke karamar hukumar Kanam a jihar Filato, ta bayyana cewa harin da aka kai wa talakawan da basu ji ba basu gani ba musamman a lokacin azumin watan Ramadan ya munana.

Ministan ta bayar da umarnin a kai kayan agaji cikin gaggawa da suka hada da abinci da ruwa da barguna da gidajen kwana ga ‘yan gudun hijirar da a halin yanzu ke neman mafaka a makarantar firamare ta Garga Central da ke karamar hukumar Kanam ta jihar Filato, ta sanar da cewa kayayyakin agajin na kan hanyar zuwa. ana kai wa za’a kawo wa waɗanda abin ya shafa.
Wasu ‘yan ta’adda dauke da makamai sun kai hari a kauyuka biyar, da suka hada da Kyaram, Gyambau, Dungur, Kukawa, Shuwaka da ke karkashin hukumar Garga a ranar Litinin din da ta gabata, yayin da aka kashe mutane da dama.

Tuni hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa karkashin ma’aikatar, tare da rakiyar SEMA, da hadin gwiwar rundunar soja, da shugabannin al’umma, da ‘yan majalisar kananan hukumomi da kuma kafafen yada labarai, sun je jihar Filato domin sanin irin barnar da akayi tare da bayar da shawara ga hukumar yadda ya kamata.

Kodinetan hukumar NEMA shiyyar Arewa ta tsakiya Jos, Mista Eugene Nyelong wanda ya jagoranci tawagar ya tabbatar da cewa an fara tantancewa, da tantance wadanda abin ya shafa.
A cewar Nyelong, tantancewar da aka fara a ranar Talata 12 ga Afrilu, 2022, ta nuna hasarar rayuka, dama kuma asarar dukiyoyi.

Adadin ‘yan gudun hijirar da aka samu sun haura mututane 4800, waɗanda sun kunshi mata da kananan yara.

Ma’aikatar lafiya ta karamar hukumar, sashen bayar da agajin gaggawa a Garin Garga na bayar da tallafin magani ga ‘yan gudun hijirar yayin da, Darakta Janar na NEMA, Ahmed Mustapha Habib, yana aiki don ganin cewa ankai agajin gaggawa.

NNEKA IKEM ANIBEZE
SA MEDIA
13-04-2022

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here