Dandalin Ci gaba da Farfaɗo da Tafkin Lake Chad Ya Samar da Dabaru Don Samun Kwanciyar Hankali a Yankin

An kammala taron yini biyu, kan ci gaba da farfado da yankin tafkin Chadi a Abuja, tare da yin ƙira ga dukkannin masu hannu da su tashi tsaye don sake gina al’umma, da al’ummar yankin tafkin Chadi da ke fama da tashe-tashen hankula da sauran matsaloli.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bada tabbacin a jawabin da ya gabatar a wajen bude taron raya tafkin Chadi a ranar Litinin da ta gabata, a babban dakin taro na kasa dake Abuja, cewa gwamnatin tarayya za ta kasance mai taka rawar gani wajen aiwatar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar. za a sa himma matuƙa wajen sake gina yankin.

Farfesa Osinbajo ya mika godiyarsa ga ministar harkokin jin kai, agaji da inganta rayuwar al’umma Sadiya Umar Farouq, da hukumar raya yankin arewa maso gabas, da hukumar kula da tafkin Chadi da sauran masu ruwa da tsaki bisa jajircewa da gudunmawar da suke bayarwa, wajen farfado da yankin tafkin Chadi, ya bada shawara cewa. Ya Kamata ayi a mika sakamako da shawarwarin dandalin ga gwamnatoci daban-daban domin jagorantar tsara manufofi, da matsaya da za a dauka kan batutuwan da suka shafi ci gaban yankin.

“Ina so in tabbatar wa dukkan abokan aikinmu cewa, gwamnati ta kuduri aniyar yin aiki tare da ku, don dorewar yankin, zaman lafiya ba tare da tashin hankali ba. Har ila yau ina so in tabbatar muku da kudurinmu na ganin cewa mun magance rikici, da sake gina rayuwar mutanen da rikicin ya shafa a yankunan. Ina da yakinin irin yadda gwamnatocin Kamaru, Chadi da Nijar suna tare damu akan irin wannan aikin, kamar yadda suka nuna a nan.

“Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta kasance mai taka rawa wajen ƙoƙarin inganta rayuwar ‘yan uwanmu, dake fadin kasashen hudu”, in ji mataimakin shugaban kasar.

Bada jimawa ba, minista Sadiya Umar Farouq ta bayyana cewa kimanin mutane miliyan 23 ne waɗanda da rikicin Boko Haram ya shafa, suka makale a cikin kasashe hudu da ke makwabtaka da tafkin Chadi a cikin shekaru goma da suka gabata.

Ministan wanda ta samu wakilcin babban sakatare, Bashir Nura Alkali, ya bayyana cewa makasudin kaddamar da taron shi ne, don ayi amfani da nasarorin da aka samu a ayyukan sojojin Najeriya da na hadin gwiwa sojojin kasa da kasa (MNJTF), dama dukkanin sojojin kasashen LCB.

“Don guje wa wasu annoba, manufarmu ita ce samar da dabarun aiki da hanyoyin magance matsalolin sauyin yanayi, da rikice-rikice, tallafawa farfado da tattalin arziki, gyara kwangilar zamantakewa da kuma magance bukatun mata, matasa da kuma masu rauni a yakunan tafkin na Chadi.

“Wannan taron ya zo daidai lokacin da yake da mahimmanci, a lokacin da muke shirin tsawaitawa fiye da kasancewar dandamali, bin burin aiwatar da ayyukan bayar da shawarwari na hadin gwiwa, ba da gudummawa ga tsari da mutuntaka, da kuma taimakawa wajen neman mafita mai dorewa a yakin tafkin Chadi”.

A rana ta biyu na taron, an gudanar da taron workshop kan ‘Mafita don jurewa yanayi a yankin tafkin Chadi’, ‘Tallafawa kananan hukumomi a yankin tafkin Chadi’ da ‘karfafa ‘yan kasa, Mata da Matasa don Gina Hadin Kan Al’umma a yakin Tafkin Chadi.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnatocin kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar da ministoci da gwamnoni da jakadu da manyan kwamishinoni da wakilan hukumomin tsaro da hukumomin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin farar hula da sauran manyan baki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here