Minista Sadiya Farouq da Tasirin Manufofin Jin Kai na Gwamnatin Tarayya

 

Ma’aikatar kula da Harkokin jin kai, agaji da inganta rayuwar al’umma, ta kasance kan gaba wajen tabbatar da manufofin jin kai na gwamnati ya isa ga al’umma, Sai dai abin da ya fi daukar hankalin jama’a shi ne yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Sadiya Umar Farouq ta sa ido a ma’aikatar da kuma hada kan ma’aikatar, an yaba da yadda ma’aikatar ke gudanar da ayyukan jin kai, ERE-EBI AGEDAH IMISI ta yi nazari kan ayyukan da ma’aikatar ke isarwa.

Kamar yadda sunan ma’aikatar ke nuni, Ma’aikatar kula da harkokin jin kai, agaji da inganta rayuwar al’umma, An kirkiro ma’aikatar ne saboda bukatar gwamnatin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan mayar da hankali wajan, daidaito, aiki tare, kafa hukuma da kuma samar da daidaituwar duk ayyukan jin kai da zamantakewa na gwamnati.

Abin takaicin shine, ganin cewa kasar na fuskantar matsaloli iri-iri, kama daga, ta’addanci a Arewa maso Gabas, tashe-tashen hankulan ‘yan fashi a yankunan Arewa maso Yamma, rikicin kabilanci da ba’a taba ganin irinsa ba a yankunan jihohin da ke tsakiya, da sace-sacen mutane, rikicin manoma da makiyaya, barkewar gobara, duk waɗannan sun haifar da gagarumin ƙira da akawo agaji.

Ƙirƙirar ma’aikatar a shekarar 2019 wanda ya kasance shine ginshikin tabbatar da cewa manufofin jin ƙai na gwamnati sun karkata zuwa ga mutanen da ke rayuwa a cikin wani yanayi acikin al’ummar mu. abin da ya fi daukar hankali shi ne yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Sadiya Umar Farouq ta sa ido a ma’aikatar da kuma hada kan ma’aikatar, an yabawa ma’aikatar bisa yadda take gudanar da ayyukan jin kai,

Kamar mace mai aiki ne wanda ta fahimci albasarta, kuma bata shiryawa kowane irin ƙwayar shagala ba, ita ba kamar sauran manyan jami’an gwamnati bane, ta kasance ba ta shakkar ganawa da masu ruwa da tsaki, musamman kafafen yada labarai, MDAs, CSOs da kungiyoyi masu zaman kansu, sun yi alfahari da tsabtatacciyar nasarorin da ta samu tun lokacin da ta karbi mukamin ministar, jagora mai kula da ma’aikatar, a kowane damar da ta samu ta kan burge masu sauraronta, har ma ana kiran ta da “star girl” na gwamnatin Muhammadu buhari zaku yi gaskiya.

Shugabancinta ya samar da tsarin da ya dace wanda ya tabbatar da cewa an yi wa ’yan kasarmu maza da mata waɗanda suka rasa matsugunnansu sakamakon kalubalen tsaro a sassan kasar, an kula dasu yadda ya kamata, duba da shekaru na rashin kulawa, watsi, da rashin gaskiya, Inda wasu marasa kishin kasar suka yi amfani da damar da irin halin da ‘yan gudun hijira suka shiga, ta hanyar satan dukiyan al’umma, da satar kudin da gwamnati ta fitar musu. Sai ga sabuwar jami’a ta zo, da kwarin gwiwa ta kuma take kafarta, ta kuma tabbatar da cewa ta lalata irin wannan aikin da aka saba yin sa a baya. Ayyuka kama Daga Borno, Adamawa, Zamfara, Yobe, Benue da sauransu, a matsayinta na uwa ta tabbatar da cewa daga cikin waɗannan nau’in ‘yan kasar da suka samu kansu a cikin wani hali, an ba su isasshen abinci da kuma rayuwa daidai gwargwado.

Wani abin ban sha’awa, bayan samar da ayyukan jin kai na yau da gobe ga ‘yan gudun hijira, wanda ya tabbatar da cewa ba su dawwama sosai ba. a wani taron da ya gabata a baya wanda aka yi a Abuja, don bikin bude ‘Humanitarian Open House’ wanda wani shiri ne na sadarwa na ma’aikatar, taron ya hada abokan hulda da masu ruwa da tsaki akan dabarun. Ministar a wani albishir mai daɗi ta farantawa masu sauraronta, a wani kafaffen dandali masu fa’ida, don samar da taimako mai ɗorewa ga ‘yan gudun hijira a duk faɗin ƙasar. Ta kaddamar da manufar kasa kan IDP, wanda ke neman samar da wani tsari, na alhakin kasa don rigakafi da kare ‘yan kasa da kuma baƙi daga abubuwan dake faruwa na son rai, da sauran su, a yayin gudun hijira, don biyan bukatunsu da basu kariya a lokacin hijira.

Har ila yau, a cikin takardar akwai taswirar hanya don tabbatar da gyara, dawowa, sake haɗewa, da sake muhalli bayan ƙaura. A cewar Ministan, manufar ta fito da ka’idojin da za su jagoranci taimakon jin kai, da kuma aiwatar da hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar gudun hijira a cikin gida Najeriya.

Karkashin Ministan mai son samun sakamako, gwamnatin tarayya ta aiwatar da National Social Investment Programme, NSIP, ana kyautata zaton shi ne shirin kare al’umma mafi girma a tarihin Najeriya da ma bayansa. Shirin ya kawo buri ga dubun iyalai ta hanyar rage radadin talauci, inganta rayuwar matasa, samar da ayyuka ga matasa, inganta ilimi, ayyukan kiwon lafiya, rage matsalar karancin abinci mai gina jiki a tsakanin yaran da suka isa makaranta, da kuma samar da hanyoyin da za a bi. zuwa wuraren bashi masu araha don kananan kasuwanci da sauransu.

Shirin N-Power, shirin National Home-Grown School Feeding Nationwide, shirin Conditional Cash Transfer, dama shirin Government Enterprise and Empowerment Programme, GEEP duk tsare-tsare ne na taimakon jama’a da ‘yan Nijeriya suka ci gajiyar su a karkashin shirin National Social Investment Programme, NSIP.

A shekarar 2020 kadai, ma’aikatar karkashin jagorancin Sadiya Umar Farouq a wani bangare na kokarin da take yi na tsamo miliyoyin matasan mu daga sana’ar kwadago, ta yadda su kansu zasu zama masu daukar ma’aikata, anyi nasarar yaye mutane 500,000 daga rukunin BATCH A da B na masu cin gajiyar shirin N-Power yayin da ake sarrafa masu neman shiga shirin sama da miliyan 6.4 na Batch C. Yana iya ba ku mamaki sanin cewa daga Batches A & B, jimlar mutane 109,823 da suka ci gajiyar tallafin sun ƙaddamar da kasuwanci a cikin al’ummominsu, wannan na nuna muhimmancin shirin N-Power.

A halin yanzu, a karkashin Batch C, Stream 1, ‘yan Najeriya waɗanda basu gaza ƙasa da mutum 510,000 ne suka yi rajista a fadin kasar, kuma suke cin gajiyar shirin, yayin da karin waɗanda za su ci gajiyar shirin za su kai kimanin mutane 490,000, biyo bayan amincewar da shugaban kasa ya yi na kara adadin zuwa miliyan daya. Abin da wannan labari mai dadi ke nunawa shi ne, kamar yadda Ministan ta bayyana karara a lokacin da masu ruwa da tsaki suke gudanar da taron shi ne, za a samar wa matasa miliyan daya sana’o’in dogaro da kai, a fannoni daban-daban nan da shekara daya, ta hanyar sana’ar hannu da kuma ba da horo, da horar da su. da gogewa, ta yadda za su iya samun kayan aiki don fara kasuwancinsu, ko amintattun ayyukan sakamakon gogewar da za su samu acikin shirin.

Yau a Nijeriya, kusan ko ina acikin al’umma akwai dillalan kuɗaɗe masu POS, ci gaban da ba wai kawai ya taimaka wajen kame al’ummar da ba su da banki bane, da kawo ayyukan kuɗi ba tare da la’akari da inda suke rayuwa ba, hakan ya jawo hankalin matasanmu. Godiya ga shirin hukumar kudi ta wayar salula na ma’aikatar. shiri ne na ƙasa baki daya a karkashin shirin N-Power an horar da jami’ai 1,850 tare da samar musu da kayan aiki, waɗanda adadinsu ya kai kimanin mutum 50 a kowace jiha tare da basu kayan aikin da ake bukata, kayan aikin sun haɗa da (POS) tare da jarin kuɗi N20.000, na’urar daukar hoton yatsa, kujerun filastik, tebur na filastik, laima, da littafin rubutu dan ajiye lissafi.

Bugu da kari, shirin ciyar da makarantu na kasa, ya fara aiki a jihohi 35 da kuma babban birnin tarayya Abuja, tare da shirye-shiryen Bayelsa, a matakin ci gaba, ba iya babban taimako bane ga iyaye da masu kula, har ma da wani gagarumin tallafi na shiga makaranta, An ƙaddamar da shirin a shekarar 2016, shirin na ba da abinci mai gina jiki sau ɗaya kyauta ga yaran dake makarantar firamare yan aji 1-3 na makarantun gwamnati a faɗin ƙasar. Waye za a tilasta masa ya je ya yi karatu ya dawo gida a koshe? A halin yanzu, kusan yara miliyan 10 ne a makarantu 54, 619 ne ke cin gajiyar wannan shirin da aka ƙirƙiro. Baya ga wannan kuma, ga masu dafa abinci 120,000, da kananan manoma kusan 100,000, da mutane masu tarin yawa, suna cin gajiyar shirin a fadin kasar. Ba da dadewa ba ma’aikatar ta yi nazari kan farashin ciyar da kowane yaro daga Naira 70 zuwa Naira 100 a kowane abincin yaro daya.

Jajircewarta a wannan ma’aikatar a cikin shekaru uku da suka gabata ya kasance tarihi acikin al’ummar Najeriya cikin kowane zamani, matsayi, yanki da addini suna matukar godiya a gare ta, ba iya uwargida Sadiya Umar Farouq kadai ba. Har da Tawagar ban mamaki na ma’aikatar, da mai girma shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatin tarayya.

Duk da cewa iya wannan yayi ƙadan da ya nuna sawun martabar da ma’aikatar ta samu a cikin kankanin lokaci, yana da kyau a lura da cewa shirin (Government Enterprise and Empowerment) wato GEEP wanda ke neman magance kalubalen bayar da lamuni da hada-hadar kudi, Sama da ‘yan Najeriya miliyan 37 waɗanda ke cikin wani hali dangane da tattalin arziki, waɗanda ke gudanar da harkokin kasuwanci, amma ba su taba samun damar samun bashi da lamuni ba zuwa yau, an bayar da karin lamuni tsakanin N10,000 zuwa N300,000 ga kusan ‘yan kasuwa miliyan 2.3 da suka amfana. , masu sana’ar hannu, matasa masu hannu da shuni, ma’aikatan gona da sauran masu samar da ayyukan yi a karkashin shirye-shiryenta na TraderMoni, MarketMoni da FarmerMoni, wanda ke ƙarƙashin kulawar ofishin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo kai tsaye.

Tasirin ya kasance abin ban mamaki, yayin da shaidar ke sanya farin ciki. TraderMoni na kula da talakawa da matasa masu sana’o’i, yayin da MarketMoni ke kula da matalauta da mata ‘yan kasuwa, kuma dukkanin bangarorin biyu suna bayar da Naira 50,000 ga kowane mai cin gajiyar shirin. Anfi mayar da hankali kan talakawa da manoman karkara a karkashin FarmerMoni, kuma kudin lamunin ya kai N300,000. Hakanan GEEP yana haɓaka haɗar kuɗi ta hanyar masu cin gajiyar shirin shiga cikin tsarin hada-hadar kuɗi na banki.

Ba zai zama kyakkyawan fata ba, don fatan cewa kwanaki masu zuwa, akwai damammaki masu yawa ga al’ummar Najeriya, saboda ma’aikatar ba iya a shirye take don ci gaba da ɗaukar shirye-shiryen ta ba, face don faɗaɗa hangen nesa, tabbatar da cewa yawancin ‘yan Najeriya sun sami karfin tattalin arziki. da kuma kula da zamantakewar jama’a, ingantaccen yanayin rayuwa a cikin aminci da tsaro saboda wannan shine hangen nesa da gwamnatin tarayya keyiwa ‘yan ƙasar

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here