Mun yi Allah Wadai da Gungun Masu Jajayen Huluna “Kwankwasiyya” – Benson Anya
A ranar Laraba 20 ga watan Satumba ne aka yanke hukuncin kotu a shari’ar zaben gwamnan Kano.
Hukuncin ya tsige Gwamna Abba Kabir tare da tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zabe.
Daya daga cikin alkalan da su ka yanke hukunci, Benson Anya ya bayyana yadda ‘yan ta’addan Kwankwasiyya su ka kore su a Kano.
Jihar Kano – Alkalan da su ka yanke hukunci a kotun sauraran kararrakin zaben gwamna a Kano sun yi martani kan barazanar da aka musu.
Alkalan sun bayyana yadda ‘yan ta’addan siyasar Kwankwasiyya masu jajayen huluna su ka kore su a Kano, TRT Afirka ta tattaro.
Meye alkalan ke zargin ‘yan Kwankwasiyya?
Sun bayyana cewa tun kafin yanke hukunci ‘yan Kwankwasiyya ke ta faman barazana ga alkalai kan shari’ar.
Read Also:
Wannan na zuwa ne bayan yanke hukuncin kotun da ta bai wa Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC nasara a zaben.
Kotun ta kuma tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP daga kujerarsa ta gwamna, The Nation ta tattaro.
Daya daga cikin alkalan da su ka yanke hukunci a kotun, Benson Anya ya caccaki ‘yan Kwankwasiyya masu jajayen huluna kan barazanar da su ka musu.
Wane korafi alkalan su ka yi kan ‘yan Kwankwasiyya?
Ya ce bai kamata ‘yan Kwankwasiyya su yi amfani da jita-jita a kafafen sadarwa da ke cewa ba za su yi nasara ba, su na barazana ga jama’a.
A cewarsa:
“Bai kamata a razana siyasar jihar Kano baki daya ba da tarzoma, Kada jam’iyya ta kuskura ta yi wa jama’a barazana da ta’addanci da tashin hankali.
“Kada a dauki hukuncin kotu da zafi wanda har zai sa a kai hari kan ma’aikatan kotu, kamar yadda wakilan wadanda ake kara su ka yi tun kafin yanke hukuncin.”
Benson ya kara da cewa:
“Mun yi Allah wadai da gungun masu jajayen huluna masu kama da ‘yan ta’adda, wadanda su ka kore mu a Kano tare da barazana ga rayukanmu.”