Shugaba Tinubu ya Umarci Jami’an Tsaro su Kuɓutar da Sauran ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau

 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’an tsaron ƙasar su kuɓutar da sauran ɗalibai mata na Jami’an Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara da masu garkuwa da mutane suka sace.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya yi Allah wadai da sace ɗaliban da aka yi ranar Juma’a, yana mai cewa wannan abu ne na rashin tausayi da imani kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Yayin da shugaban ya jajanta wa iyalan waɗanda aka sacen, ya tabbatar da cewa a shirye gwamnatinsa take wajen kare duka ‘yan Najeriya, yana mai alƙawarta cewa za a yi duk mai yiwuw domin kuɓutar da ɗaliban.

Haka kuma shugaban ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar da bayar da kariya ga makarantu kasancewarsu cibiyoyin bayar da ilimi da ci gaban al’umma.

A ranar Juma’a da daddare ne wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai suka dirar wa ɗakunan kwanan ɗaliban da ke unguwar Sabon-Gida tare da sace ɗalibai galibinsu mata, sai dai daga baya rahotonni sun ce an kuɓutar da wasu daga cikinsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com