Premier League: Chelsea ta yi Rashin Nasara da ci 1-0 a Hannun Aston Villa

 

Chelsea ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Aston Villa a karawar mako na shida a Premier League ranar Lahadi.

Ollie Watkins ne ya ci kwallon sauran minti 13 a tashi daga wasan da suka fafata a Stamford Bridge.

Chelsea, wadda ba ta buga gasar Zakarun Turai a bana, bayan da ta kammala a mataki na 12 a bara ta karasa wasan da ‘yan kwallo 10 a fili, bayan da aka bai wa Malo Gusto jan kati.

Wasa na uku da aka ci Chelsea a bana da canjaras biyu, yayin da karawa ɗaya Pochettino ya ci tun bayan da ya karɓi ragamar kungiyar a bana.

Chelsea ta doke Luton 3-0 ranar 25 ga watan Agusta a fafatawar mako na uku a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Villa ta yi rashin nasara da ci 3-2 a gasar zakarun Turai ta Europa League, wadda ta ci wasa na huɗu daga shidan da ta fafata a kakar nan.

Wasan da aka doke Villla shi ne a gidan Newcastle United da wanda ta yi rashin nasara a hannun Liverpool.

Kafin wasan na ranar Lahadi, Chelsea ta doke Aston Villa karo 13 daga fafata 17 baya a Premier League.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com