Tsohon Gwamnan Ribas na Shirin Kwato Harkokin Siyasar Jahar – Chibuike Amaechi

 

Chibuike Amaechi na shirin dawowa da karfi domin kwato harkokin siyasa a jahar Ribas a 2021.

Tsohon gwamnan na jahar ya bugi kirjin cewa idan ya dawo, zai murza kambun domin duk abunda ya fadi zai kasance haka.

A cewar Amaechi, shi baya kabilanci wanda hakan ne dalilin da yasa yayi aiki don nasarar shugaba Buhari a 2015.

Ministan sufuri, Chuibuke Amaechi, ya ce ya zabi kasancewa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015 maimakon Gooduck Jonathan saboda shi baya nuna kabilanci.

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya yi ikirarin cewa Jonathan ya gabatar masa da kawara daban-daban don ya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), amma ya ki amsa tayinsa.

Ya ce a lokacin da ya bar jam’iyyar, tsohon Shugaban kasar yayi fada da shi amma ya yi nasarar shawo kan lamarin saboda Allah na tare da shi.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Amaechi ya bayyana hakan ne yayinda ya tarbi wasu mambobin PDP da suka sauya sheka zuwa APC a Port Harcourt.

A cewar tsohon gwamnan, zai koma jihar mai albarkar man fetur a 2020 don komawa ga harkokin siyasa, sannan idan yayi hakan, zai dunga jagorantar duk wani harkoki a jihar.

Ya kara da cewa duk abunda ya fadi shine zai faru. Ya kara da bayyana cewa bai taba shan giya ba a rayuwarsa, sannan bai taba shan sigari ba kuma shi baya nuna kabilanci.

Amaechi ya kara da cewa: “Da ina da kabilanci, shugaba Goodluck Jonathan ya gabatar mani da dama don ci gaba da kasancewa a PDP.

Ya gabatar mani da duk wasu damammaki, amma na bayyana cewa nab a Buhari goyon bayana saboda ni bana kabilanci.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here