Cross River: INEC ta sanar da Jam’iyyar da ta Lashe Zaben Cike Gurbin Sanata

Hukumar INEC ta kaddamar da dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na Sanata a Cross River ta arewa.

Baturen zaben, Farfesa Ameh Akoh ne ya sanar da hakan a yau Lahadi, 6 ga watan Oktoba.

Dr Stephen Odey ya samu kuri’u 129,207 wajen kayar da sauran yan takara takwas da suka fafata da shi.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, ta kaddamar da dan takarar jam’iyyar of People’s Democratic Party (PDP), Dr Stephen Odey, a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na sanata mai wakiltan Cross River ta arewa.

An dai gudanar da zaben cike gurbin ne a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba. Baturen zaben cike gurbin, Farfesa Ameh Akoh na jami’ar tarayya ta Alex Ekwueme, Ikwo, jihar Ebonyi, shine ya sanar da sakamakon zaben, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Ya ce dan takarar PDP, Dr Stephen Odey ya samu kuri’u 129,207 wajen kayar da sauran yan takara takwas.

A cewarsa, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Mista Joe Again (SAN) ya samu kuri’u 19,165 wajen zama na biyu.

Sannan kuma dan takarar African Democratic Congress, Mista Gregory Agam ya zo na uku da kuri’u 388.

“An kaddamar da dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe daidai da gudanarwar zaben bayan ya samu kuri’u mafi yawa,” in ji shi.

Hakazalika, Misis Maria Akwaji ta lashe zabe a zaben cike gurbi na mazabar Obudu ta jiha bayan ta samu kuri’u 32,166 wajen kayar da abokin hamayyarta, Mista Abor Adaji na APC wanda ya samu kuri’u 3,546.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here