BUK: Farfesa Ali Muhammmad garba ya Rasu

Jami’ar Bayero da ke Kano ta sake yin rashin babban malami, Farfesa Ali Muhammad Garba a ranar Lahadi.

Farfesa Ali ya rasu Kwanaki biyu kacal bayan ya wallafa, a shafinsa dandalin sada zumunta, cewa ya na neman addu’a a wurin jama’a.

Marigayin ya shiga jerin manyan malamai ma su mukamamin Farfesa da BUK ta rasa a cikin shekarar nan.

Farfesa Ali Muhammad na sashen koyar da ilimin kasuwanci a jami’ar BUK ya rasu, kamar yadda Legit.ng Hausa ta tabbatar.

A ranar Juma’a, 4 ga watan Disamba, ne Farfesa Ali ya wallafa cewa ya na neman jama’a su taya shi da addu’a saboda an kwantar da shi a asibiti.

Bayan ya yi sallama irinta addinin Musulunci a shafinsa na Facebook, Farfesa Ali ya bayyana cewa, “To, wankin hula ya kaimu dare.

“Bayan zazzafar muhawara da fada da kusan dukkan iyalina, an kwantar da ni a asibitin UMC Zahira da ke Kano.

“Yanzu ba ni da halin yin mahawara ko musu koda ta hanyar latsa makulan kan wayata ta hannu.

“Ku taimaka, ku sakani a cikin addu’o’inku.” Marigayin ya shiga jerin Farfesoshi da jami’ar BUK ta rasa a cikin shekarar nan.

Daga cikinsu akwai Farfesa Haruna Wakili Wanda ya rasu a watan Yuni, Farfesa Monsuru Wanda ya rasu a watan Mayu, da kuma Farfesa Balarabe Maikaba wanda ya rasu a watan Afrilu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here