Endsars: Wata Jaha ta Dawo da Zanga-Zangar

Matasa sun fara gudanar da sabuwar zanga zangar EndSARS a garin Osogbo, jahar Osun.

Sun gudanar da gangamin ne a yau Litinin, 7 ga watan Oktoba inda suka yi tattaki har zuwa majalisar dokokin jahar.

Masu zanga zangar da ke kira ga shugabanci nagari da wasu bukatun sun nemi zantawa da shugabannin majalisar.

Wasu matasa karkashin inuwar gangamin #EndSARS, a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, sun gudanar da zanga zangar a Osogbo, babbar birnin jihar Osun.

Sun yi gangamin ta cikin unguwannin Osogbo zuwa majalisar dokokin jihar Osun, inda suka bukaci tattaunawa da shugabannin majalisar, jaridar Punch ta ruwaito.

Zanga zangar wanda Emmanuel Adebisi ya jagoranta na kira ga shugabanci nagari da sauran abubuwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here