Ambaliyar Ruwa ta Kashe Mutane 20 a Koriya ta Kudu

 

Akalla mutum 20 ne suka mutu, sannna aka kwashe wasu dubbai, bayan da wata mummunar ambaliya ruwa ta afka wa Koriya ta Kudu sakamakon mamakon ruwan sama a yankunan tsakiyar ƙasar.

Ruwan sama mai ƙarfi da aka kwashe tsawon kwana uku ana tafkawa a ƙasar ya haifar da zaizayewar laka tare da cikar babbar madatsar ruwa da ke lardin arewacin Chungcheong, lamarin da ya sa ta batse.

Mamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske ya haddasa karyewar titunan mota, da na hanyoyin jiragen ƙasa, inda ya rika tafiya da ƙananna motoci.

Jami’ai sun ce an tilasta wa dubban mutane barin gidajensu, yayin da mutum 14 suka ɓata.

Lardin Arewacin Gyeongsang mai tsaunuka ne lamarin ya fi ƙamari, inda zaizayewar laka ta haddasa lalacewar gidaje masu yawan gaske.

Firaministan ƙasar Han Duck-soo ya buƙaci sosjojin kasar su taimaka wa aikin ceto.

Hukumomi sun ce ƙananan motoci 19 ne ruwan ya tafi da su a lardin Chungcheong da ke tsakiyar ƙasar, lamarin da ke haddasa fargabar ƙaruwar adadin waɗanda suka mutu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here