Yadda Jihata ke Tafka Asarar N10bn a Duk Ranar Litinin ta Kowace Mako – Gwamna Mbah

Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya ce jiharsa na tafka asarar kuɗi biliyan N10bn a duk ranar Litinin ta kowace mako.

Mbah, mamban jam’iyyar PDP ya ce Enugu na rasa waɗan nan kuɗin ne sakamakon dokar zaman gidan da IPOB ta ƙaƙaba.

Ya ce babu wata dokar zaman gida, ya kamata mutane sun fahimci cewa bai kamata su na yi wa wasu tsirarun mutane biyayya ba.

Enugu – Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya ce dokar zaman gidan da ƙungiyar ‘yan aware IPOB ta ƙaƙaba a Kudu maso Gabas, tana jawa jiharsa asarar makudan kuɗaɗe.

Gwamnan ya yi ikirarin cewa a kowace ranar Litini da dokar ke aiki, jihar Enugu na tafka asarar kuɗi kimanin biliyan N10bn, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Peter Mbah ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Enugu a wurin taronsa da shugabannin garuruwan da ke cin gashin kansu.

Ya ce jihar na asarar wannan makudan kuɗin ne sakamakon hana gudanar da harkokin kasuwanci da tattalin arziƙi a kowace ranar Litinin saboda haramtacciyar dokar zaman gida.

The Cable ta rahoto gwamnan na cewa:

“Yana da amfani mu san dangantakar talauci da wannan dokar da ake kira zaman gida. Duk ranar Litinin din da muka zauna a gida muna rasa N10bn saboda hana harkokin arziki a nan jihar mu.”

“Duk mutanen da suka zauna a ɗakunan Otal-Otal da niyyar sai ranar Litinin zasu tafi, yanzu dole su ke sauya shawara ba zasu wuce ranar Lahadi ba, me ya faru kenan? Masu Otal sun rasa kuɗin shigar da zasu samu a ranar.”

The Cable ta rahoto gwamnan na cewa: “Yana da amfani mu san dangantakar talauci da wannan dokar da ake kira zaman gida. Duk ranar Litinin din da muka zauna a gida muna rasa N10bn saboda hana harkokin arziki a nan jihar mu.”

“Duk mutanen da suka zauna a ɗakunan Otal-Otal da niyyar sai ranar Litinin zasu tafi, yanzu dole su ke sauya shawara ba zasu wuce ranar Lahadi ba, me ya faru kenan? Masu Otal sun rasa kuɗin shigar da zasu samu a ranar.”

Ya kamata mutane su fahimci babu wata dokar zaman gida – Mbah

A cewarsa, tabarɓarewar tsaro da dokar zaman gida ka iya kawo wa kudirinsa na inganta tattalin arzikin jihar Enugu cikas.

Gwamna Mbah ya roki shugabannin da su koma su ja hankalin mutanensu kuma su fahimtar da su cewa babu wata dokar zaman gida ranar Litinin ko wata rana daban.

Mbah ya tabbatar wa al’umma cewa hukumomin tsaro suna da bayanin komai, zasu tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin mutanen Enugu.

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here