Ambaliyar Ruwa: Al-Umma da Dama Sun Rasa Gidajensu da Dukiyoyinsu a Jihar Kano
Ambaliyar ruwa ta rusa gidaje masu yawa a ƙauyuka da dama a yankin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da ke jihar Kano, arewa maso yammacin Najeriya.
Mamakon ruwan sama da ake yi a kwanaki da dama a jere ne ya yi sanadiyyar ambaliyar tare da rushewar gidajen.
A yankin ƙaramar hukumar Ajingi ma an sami asarar rayuka tare da asarar dukiyoyi masu yawa.
Haka zalika ginin wata makaranata ya faɗa wa wasu ƴan makaranta wanda ya yi sanadiyar mutuwar ɗaya daga cikinsu.
Read Also:
Yankuna da dama a Kano dama wasu jihohi a arewacin Najeriya na fuskantar ambaliyar ruwa, saboda mamakon ruwan sama da ake fuskanta a damunar bana.
A makon da ya gabata an shafe kwana uku a jere ana tafka ruwan sama, babu ƙaƙƙautawa, wanda hakan ya shafi harkokin kasuwanci da matsugunan al’umma.
A kauyen Shuwawa da ke yankin Danbagina a Dawakin Kudu, da dama daga cikin mazauna ƙauyen sun bar gida, inda suka tura iyalansu gidajen iyayensu, kamar dai yadda Malam Garba Dawa ya shaida wa BBC.
Malam Garba ya ce ambaliyar ta rushe gidansa tare da lalata masa amfanin gonarsa baki daya.