Mun Amince za mu yi Aiki da Yarjejeniyar Taiwan – Shugaba Biden
Shugaba Biden ya ce ya yi magana da takwaransa na China Xi Jinping game da Taiwan, yayin da ake ci gaba da samun fargaba sakamakon shawagin jiragen saman sojojin China kusa da tsibirin.
Read Also:
Mista Biden ya ce sun amince za su yi aiki da yarjejeniyar Taiwan – wata alama da ke nuni da cewa Chinar ba za ta yi amfani da karfi wajen kwace Taiwan ba.
Rahotanni na cewa duk wani rikici a mashigin na Taiwan na iya haifar da yaƙi da Amurka a yankin ko ma duniya baki daya.
Idan anjima ne ake sa ran mai bai wa shugaba Biden shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan zai tattauna da babban jami’in diflomasiyyar China Yang Jiechi a Geneva.