Ba za su Amince a Riƙa Kaɗa Tutar Wata ƙasa ba a Najeriya – Shugaban Hafsan Tsaro

 

Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Christopher Musa ya ce ba za su amince a riƙa kaɗa tutar wata ƙasa ba a Najeriya.

Christopher Musa ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da suka yi da shugaba Bola Tinubu a yau Litinin.

An ga masu zanga-zanga da dama na ta ɗaga tutar Rasha bayan fitowa domin nuna adawa da tsadar rayuwa da ake ciki a ƙasar.

Ya ce lokacin da zanga-zangar ta fara ta kasance ta lumana, sai dai wasu ɓata-gari na ƙoƙarin shiga cikinta domin tayar da tarzoma.

“Dukkanmu mun ga yadda ɓata-gari suka shiga cikin zanga-zangar, inda aka yi ta sace-sace da kuma aikata abubuwan da ba su dace ba,” in ji babban hafsan tsaron.

Ya ce ba za su zuba ido su ci gaba da kallon yadda masu zanga-zangar ke ta ɗaga tutocin Rasha ba.

“Muna gargaɗi da babbar murya, kuma shugaban ƙasa ya ce mu faɗa muku cewa, ba za mu amince da duk wani da ke ɗaga tutar wata ƙasa ba a Najeriya. Yin hakan cin amanar ƙasa ne,” in ji Musa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here