Amurka za ta ci Gaba da Taimakawa Al’ummar Afghanistan – Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce sun bude wani shafi a Afghanistan wanda kasarsa za ta yi amfani da diflomasiyya wurin kawo mata ci gaba.
Mr Blinken ya ce idan har za su iya aiki kafada da kafada da Taliban domin ganin ci gaban Afghanistan to a shirye suke.
Read Also:
Antony Blinken ya ce Amurka za ta ci gaba da taimakawa al’ummar Afghanistan da kayan more rayuwa, amma ta hannun kungiyoyin agajin kasa da kasa ba Taliban ba.
Idan anjima ne Shugaba Joe Biden zai yi wa al’umma jawabi kan matakinsa na kawo karshen yaki a Afghanistan.
Tunda farko Majalisar Dinkin Duniya ta aminta da kudurin hana Taliban ba da mafaka ga yan ta’adda, tare kuma da martaba ‘yancin mata da tsiraru.